DA ME ZA MU FUSKANCI RAMADAN? 03

*DAME ZAMU FUSKANCI RAMADAN???*
*003*

DAME ZA MU FUSKANCI RAMADAN ?
Yana daga cikin halin magabata na qwarai sun kasance suna addu‟a watanni da dama kafin zuwan Ramadan Allah ya riskar dasu watan Ramadan da Imani, ba wannan addu‟a ba ka dai suke yi, bal sun kasance suna tanadin zuwansa ta hanyar aiwatar dasu ayukka. Kadan daga cikin ababen da Magabata sukeyi domin tanadin zuwan watan Ramadan akwai
1. TUBA NA GASKIYA
Sanin kowa ne Tuba wajibi ne akowane lokaci, sai dai saboda gabatowar 
wannan wata maigirma mai kuma albarka yana da kyau mutun ya 
gaggauta tuba akan laifukan da ya kasance yana yi tsakaninsa da 
mahaliccinsa, da kuma haqqoqin da ke tsakaninsa da mutane domin ya 
shiga wannan wata salun – alun. Allah (SWT)
Yana cewa acikin Al
-Qurani:
 .... وَتُوبُوۤا۟ إِلَى ٱللَّهِ جَمِیعًا أَیُّهَ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ.
[Surat An-Nur 31]
Haka ma Fiyayyen Halitta yana cewa “Ya ku mutane ku tuba zuwa ga Allah 
domin ni ina tuba gareshi a yini sau dari (100)” (Muslim 2702).
2. ADDU’A
Ya tabbata sashen Magabata sun kasance suna Addu‟a tsawon wata 
shidda kafin Ramadan, Allah Ya riskar dasu Ramadan, sannan kuma suyi 
addu‟a tsawon wata biyar bayan Ramadan Allah Ya karba masu ibadunsu.
Don haka ya kamata ga kowane musulmi yayi addu‟ar Allah ya riskar dashi 
Ramadan da Imani da kuma Lafiya Ya kuma bashi qwarin guiwa wajen yi 
masa Da‟a, Ya kuma roki Allah Ya karba masa.
3. YIN FARIN CIKI
(قُلۡ بِفَضۡلِ ٱللَّهِ وَبِرَحۡمَتِهِۦ فَبِذَ ٰ⁠لِكَ فَلۡیَفۡرَحُوا۟ هُوَ خَیۡرࣱ مِّمَّا یَجۡمَعُونَ)
[Surat Yunus 58]
“Kace: Da wannan falalar Allah, da RahamarSa gameda wannan suyi farin 
ciki shi yafi alkhairi daga abinda suke tarawa”
Yana daga cikin ni‟imar Allah akan bayinSa, su samu damar riskuwar
wannan wata mai albarka.
 Domin watan Ramadan wata ne mai cike da albarka, acikinsa ne ake bude kofofin Aljanna a kulle kofofin wuta akuma daure shedanu Ba qaramar ni‟ima ce ba mutun ya tsinci kansa acikin wadanda suka riski Ramadan, abun da zai kara nuna mana haka shine hadisin da Ibn Majah ya ruwaito akan wasu mutane guda uku, biyu daga cikinsu sun samu yin shahada dayan da bai mutu ba ya samu riskuwar Ramadan sannan ya mutu a shinfidarsa,amma daga karshe Annabi ya nuna wannan ya fi daraja saboda ya samun riskuwa da watan Ramadan kuma ya azumce shi har Annabi ya kwatanta tazarar da ke tsakaninsa da biyun kamar tazarar da ke tsakanin sama da Qasa.
Imamun Nawawi (Rahimahullah) yana cewa acikin littafinsa Al-Azkar:
“Ka sani, anso ga wanda wata ni‟ima ta zahiri ta jaddadu agareshi, ko kuma aka tunkude masa wani bala‟i ko Musiba,Yayi sujudar godiya ga Allah (SWT), kuma Ya gode maSa, kuma yayi yabo gareShi”
4. RAMA AZUMIN BARA(da aka biyo ka/ki)
Sanin mune wannan ibada ta Azumi wajibi ce ga kowane Musulumi baligi, Macce da Namiji. Amma duk da haka akwai wadanda sharia ta yiwa 
rangwame susha azumi daga baya sai su ranka.
Don haka yana daga cikin tanadin da za kai ga zuwan Ramadan ka yi kokari ka ranka azumin 
Ramadan da ya gabata idan ana biyanka. Musamman ma ga mata su da 
mafiyawan cinsu sukan sha azumi ta dalilin Al‟ada ko Ciki ko kuma 
shayarwa.
Kada mutun ya yarda ya yi sakaci bai ranka azumin Ramadan na Bara ba 
kuma har na Bana ya riskeshi.
Hadisi ya tabbata acikin Sahihul Bukhari (1950) da Muslim (1146) daga Abi 
Salama Yace: “Naji Aisha (RA) tana cewa rankon azumin Ramadan yana kasancewa akaina, ban samun damar ranka shi sai acikin watan sha'aban.
*MU HADU A RUBUTU NA GABA*
*ASSALAMU ALAIKUM*

Post a Comment (0)