FADAR CEWA WANDA DUK YA RIGA SANAR DA WANI RANAR DA RAMADANA ZAI SHIGA, WUTA TA HARAMTA A GARE SHI KARYA NE!


FADAR CEWA WANDA DUK YA RIGA SANAR DA WANI RANAR DA RAMADANA ZAI SHIGA, WUTA TA HARAMTA A GARE SHI KARYA NE!

https://chat.whatsapp.com/IQUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E

TAMBAYA❓

RAMADAN Zai Fara 13 ga Watan Afrilu 2021 Insha Allah.Annabi MUHAMMAD (S.A.W) Yace Dukkan Wanda Yataba Sanar da Wasu Ranar RAMADAN Wutar Jahannama ta Haramta Gareshi Ni Na Yi Nawa Don Allah Ki/Ka Sanar da Wasu Ranar Domin Suma Su Amfana.
NAGODE....,......
NAGODE..........
NAGODE..,.......

Assalaamu alaikum mallam,
Don Allah malam wannan hadisin gaskiya ne ?


 *AMSA*👇

Assalaamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillahi wa ala alihi wa sahbihi ajma'in. 

Wannan zancen jahilci ne, na 'yan son banza, masu neman lada ba tare da sun yi aiki ba. Ga zancen fa, babu sanadi ballantana marji'i duk inda zaka gan shi

قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: إذا سبق شخص بإخبار شخص آخر بالشهر المبارك حرمت عليه النار، 

Wannan zancen dake cewa, idan wani ya rigayi wani daban da labarin wata mai albarka an haramta wuta a kan shi, babu shi a cikin littafan sunnah kaf din su, kai hatta a cikin littafan da ake tattara hadisan karya da na bogi da raunana, basu zo da wannan zancen ba. Karya ce aka kirkira aka sako ta cikin addini don a nesanta mutane daga al'amura na addinin su muhimmai.

Don haka asali, yada wannan zance haramun ne ko yin nasiha, wa'azi ko tunatarwa da shi. Duk wanda yayi haka bayan ya baiyana a gare shi cewa karya aka yiwa Annabi, toh hukuncin yiwa Annabi karya, cewa ya zabi wurin zaman shi a cikin wuta, ya hau kan shi. Don haka mu kame harsunan mu da hannayen mu daga yada wannan mummunar karya a tsakanin musulmi. 

عن أَبِي هُرَيْرَةَ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: مَنْ تَقَوَّلَ عَلَيَّ مَا لَمْ أَقُلْ، فَلْيَتَبَوَّأْ مَقْعَدَهُ مِنْ النَّارِ. رواه ابن ماجه، وحسنه الألباني، وصححه شعيب الأرناؤوط.

Shi hadisin karya, kamar yadda Imam Assuyudi rahmatullahi alaihi ya kawo a Tadribur Rawiy, lokacin da yake nakalto hakan daga Imam Aljawziy, ana gane shi ta hanyoyi kamar haka

وَقَالَ ابْنُ الْجَوْزِيِّ: مَا أَحْسَنَ قَوْلَ الْقَائِلِ: إِذَا رَأَيْتَ الْحَدِيثَ يُبَايِنُ الْمَعْقُولَ أَوْ يُخَالِفُ الْمَنْقُولَ أَوْ يُنَاقِضُ الْأُصُولَ، فَاعْلَمْ أَنَّهُ مَوْضُوعٌ، وَمَعْنَى مُنَاقَضَتِهِ لِلْأُصُولِ: أَنْ يَكُونَ خَارِجًا، عَنْ دَوَاوِينِ الْإِسْلَامِ مِنَ الْمَسَانِيدِ وَالْكُتُبِ الْمَشْهُورَةِ.

Bayan wannan ma yana da kyau mu rufe da kara wani hadisin ma na karya dake cewa, musulmi su yi ma kan su tahannu'i, ko barka da arzikin ganin Ramadan ko congratulations, shi ma wannan hadisi na karya ne, ga shi kamar haka

عَنْ عُبَادَةَ بْنِ الصَّامِتِ ، أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَعَلَى آلِهِ وَسَلَّمَ قَالَ يَوْمًا ، وَحَضَرَ رَمَضَانُ:
( أَتَاكُمْ رَمَضَانُ شَهْرُ بَرَكَةٍ ، فِيهِ خَيْرٌ يَغْشَاكُمُ اللَّهُ فَيُنْزِلُ الرَّحْمَةَ وَيَحُطُّ فِيهَا الْخَطَايَا ، وَيُسْتَحَبُّ فِيهَا الدَّعْوَةُ ، يَنْظُرُ اللَّهُ إِلَى تَنَافُسِكُمْ وَيُبَاهِيكُمْ بِمَلَائِكَةٍ ، فَأَرُوا اللَّهَ مِنْ أَنْفُسَكُمْ خَيْرًا ، فَإِنَّ الشَّقِيَّ كُلَّ الشَّقِيِّ مَنْ حُرِمَ فِيهِ رَحْمَةَ اللَّهِ ) .

Wannan hadisi wasu jama'a sun ruwaito shi kuma yana littafai daban daban na sunnah, sai dai na karya ne, bai inganta ba. Na kawo wannan hadisin ne, ba don an tambaye ni ba, sai dai domin ya zamo riga-kafin yiwa Annabi karya ko yin aiki da hadisin karya da yada shi. Haka kar wani ya zo yana cewa da wanin shi, barkan mu da arziki da zuwan Ramadan da sauran su. 

Wallahu ta'ala a'lam.

 *_Amsawa_* :

 *Malam Aliyu Abubakar Masanawa*


‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)