*DA ME ZAMU FUSKANCI RAMADAN*
*006*
CIGABA....
👉🏻 *FITAR DA ZAKKA A WATAN SHA’ABAN*
Magabata sun kace sukan jawo lokacin fitar da Zakkar su zuwa watan Sha‟aban.
FAIDA anan shine domin su taimakawa Faqirai da Miskinai domin su samu qwarin guiwa aiwatar ibadar da za‟a shiga ta Azumi da Sallolin dare.
Anas bin Malik (RA) Yace: “Musulmai sun kasance idan watan Sha‟aban ya shigo za su doge wajen karatun Al-Qurani, za su fitar da Zakkar dukiyoyinsu domin karfafawa Miskinai da masu rauni akan azumin watan
Ramadan”
YANA DAGA CIKIN KUUSKURE.
Shaikh Muhammad bin Salih Almunajjid (Hafizahullah yana cewa acikin risalar da ya wallafa akan fa‟idodin watan Sha‟aban Yace: “Yana daga cikin kuskure da mafi yawan masu wadata ke yi shine, su jinkirta fitar da Zakkar su sai cikin watan Ramadan.
Alhali ba ya halatta a jinkirta fitar da zakka bayan ta kai nisabi kuma shekara ta zagayo mata. Domin yin hakan akwai zalunci ga Talakawa, kuma akwai jinkirta musu haqqinsu, wanda
hakan sabawa Allah(SWT) ne”.
*ABIN LURA.*
Sai dai yana halatta gaggauta fitar da zakka (kafin lokacinta) saboda
buqatuwar Talakawa da kuma taimaka musu.
Muhadu a darasi na gaba........
✍🏻 *Musa Yaqoub Sulaiman* *(Ibnkhasir)*
09064594611