HUKUNCIN YIN NIYYA BIYU GA MAI AZUMI


*HUKUNCIN YIN NIYYA BIYU GA AZUMI DAYA*

https://chat.whatsapp.com/Cnf26Q8MPqz9yUYU1nxqRq

*TAMBAYA*❓

Assalamu Alaikum Allah yagafartama malam Tambayana itace Karin bayani Gameda hadisn Da Akace (Innamal A,amalu binniyyat) tom mutunne Ana binshi bashin Azumi zai iya ninya biyu kamar ranan littini zai iya ninya biyu na nafila dana ramuwa

*AMSA*👇

Wa alaikumus salamu wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillahi wa ala alihi wa sahbihi ajma'in. 

Wannan mas'ala ce ta ijtihadi tsakanin Mallamai, sun kara wa juna ilmi. Inda wani sashe na su ke ganin baya halatta mutum ya zo da ibadah daya ta wakilci biyu ko ukun ta a lokaci guda duba da asali da kuma rashin nassi. Misali, ana bin mutum azumin bara da ya wuce, yanzu sai a wannan Ramadan yayi azumi daya da niyyar azumtar na wannan shekara da kuma na wanda ake bin shi na ramakon shekarar da ta gabata. Ko kuma ana bin shi bashin sallar azahar sai ya sallaci la'asar da niyya biyu, ta zamo ita ce la'asar da azahar din sa take-yanke, a lokaci guda. A nan an hada ibadodi biyu ko sama da haka a lokaci daya, cikin ibadah daya, fa niyya biyu, suka ce hakan baya halasta.

Wasu Mallaman sun tafi a kan hakan ya halasta, amma da sharadin dukkanin su ba wajibai bane, misali, ya halasta hada azumin Litinin ko Alhamis da na 13, 14 ko 15 ga wata, sai ya zamo azumi daya da niyya biyu. Haka sallar walaha da ta ramakon sunnar asuba ko sallar bullowar rana, duk biyun hukuncin su guda. 

Amma hadin gambizar da ka ambata ba zai yiyu ba domin hukuncin su ya banbanta, daya wajibi ne daya kuma mustahabbi ne, sannan babu wani nassi a kan haka, don haka barin shi, shine aula. 

Tabbas hadisin innamal a'malu bin niyyat, shine abin dogaron hukunta halascin hakan, amma kamar yadda bayani ya gabata, bai shiga cikin wajiban al'amura da kuma ababen da hukuncin su ba daya ba, ka sallaci raka'a biyu da niyyar raka'atal fajri da asuba. 

Amma kana iya hada kamar wankan Juma'a da na janaba, kayi daya. Ko shi ma wannan, ka yi biyu shi ya fi lada da inganci, domin ka yi amfani da nassi, wancan kuma yayi amfani da ijtihadi.

Wallahu ta'ala a'lam.

 *_Amsawa_* :

 *Malam Aliyu Abubakar Masanawa*

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: 👇_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)