ME CIKI KO SHAYARWA ZA TA IYA AJIYE AZUMI?


*MAI CIKI KO SHAYARWA ZATA IYA AJIYE AZUMI?*

https://chat.whatsapp.com/KeXayNmsBie671pMAKT9xN

*TAMBAYA*❓

_Shin wai gaskiyane cewa duk Mace *Mai-Ciki* ko Mai *Shayarwa* zata iya ajje azumi ta ciyar kawai amadadinsa kokuma ya abin yake??_

*AMSA*👇

_*Ko Shakka bābu* cewa wannan magana ba gaskiya bace domin kuwa bahaka *Shari'a* tace ayiba, danhaka dai da farko yana dakyau musani cewa bawai haka kawai dan saboda kasancewar Mace tana da Ciki ko tana *Shāyarwa* hukuncin yin azumi yafāɗi akantaba, domin dayawa daga cikin *'Yan'uwa Mātā* sunyiwa wannan hukunci mummunar fahimta, kodai wasu saboda *Jāhilcinsu* ko saboda son zuciya kokuma saboda ƙarancin bayani daga wajen su *Mālaman* da suke basu fatawa akan hakan, domin dayawa daga cikin *Ɗāliban-Ilimi* zaka samu suna bada fatawane kawai akan cewa *Mai-Ciki* da *Mai Shāyarwa* zasu ciyarne kadai amadadin azuminsu, wanda kuma bahaka hukuncin yake *a Sake ba Ƙaidi ba,* idan *Mai-Ciki* ko *Mai Shāyarwa* kokuma *Maras lāfiya* sunājin ƙarfin jikinsu yadda zasu iyayin azumi batare da sun galabaita irin galabaitar da *tasāɓāwa* yadda akasaba gani abisa al'āda ba, to wajibine akansu suyi wannan azumin, idan kuma sukaƙiyi to susani cewa sunbar wani wājibi da *Aʟʟαн(ﷻ)* Ya wajabta musu suyi, kuma Sai *Aʟʟαн(ﷻ)* Yākamasu da laifin hakan domin Shidai Aʟʟαн(ﷻ) baza'a iya yimasa ƙarya ko wayoba, amma idan yakasance Mutum yana cikin laulayin da idan yayi azumi zai tagayyara irin tagayyarar da yawuce na al'ada, kamar misalin Mutum yafita daga hayyacinsa ko yariƙa suma saboda wahala ko wani abu makamancin haka, kokuma yin azumin zai iya ƙāra cutar datake dāmunsa ko tayi jinkirin warkewa kokuma yakamu da wata sabuwar rashin lafiyar adalilin azumin dayayi, to anan sai *Shari'a* tayimasa rangwame akan cewa zai iya cin abincinsa, daga baya kuma idan yawarke sai yarama adadin azumin da yasha, amma ba dalili bane wai kaji Mace tace wai azumi yana bata wahala danhaka bari tasha ruwa itama bayan Sallah sai taciyar, wannan wasane da addini kawai, domin kuwa ana maganane akan irin wahalar da tasabawa irin wahalar da aka saba ji a al'ada, amma inba hakaba ai koma waye zaiyi azumi dole sai yaji ajikinsa,_
:
_Danhaka kuskurene babba Mutum yarika wasa da lamarin addininsa, Sannan wasu daga cikin Mutāne kuma sukayi wani wāyo na son zuciya, yāyin da akace *Mālamai sunyi Saɓāni akan wata Mas'ala ta Fiƙhu,* to kawai sukan dubane suga wanne ɓangarene yafi sauƙi sai su ɗauka suyi amfani dashi, ko shakka babu wannan kuskurene babba, domin kuwa idan *Mālamai* sukayi *Saɓāni* to anasone Mutum yaɗauki ɓangaren da yake da Dalilai da Hujjoji masu ƙarfi koda kuwa shine ɓangaren da yafi wahala ɗin, *Aʟʟāн(ﷻ)* Ya gānar damu gaskiya ya bāmu ikon aiki da'ita *Āmīn-Yā-Rabbi.*_
:
*_(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)_*

  *_→AMSAWA←_*
           *Mυѕтαρнα Uѕмαn*
         *08032531505*

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)