NA SADU DA MIJINA KUMA NA MAKARA DA JANABA A JIKINA, ZAN IYA AZUMI?



*SADUWA DA MIJI KUMA INASON NAYI AZUMI AMMA NA MAKARA BANYI WANKAN TSARKI DA WURI BA SAI 6am*

https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8qu9GT

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaykum. Malam ya ibada? Allah yasamu dace. Malam don Allah ina son nasan nayi sadowa da miji neh kuma inason nayi azumi ko naceh natashi da niyar azumi amma sai na makara banyi wakan tsarki da huri ba bayan sadowa ta dashi sai 6am na makara shin zan iya dauki azumi na bbu damuwa? Dan Allah ayi min bayani malam Nagode

*AMSA*👇

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Dukkan MAZHABOBIN nan hudu sunyi ittifaki
akan sahihancin azumin mai janaba ko mai hailan da batayi wanka ba.
Sai dai an ruwaito daga URWATU BIN ZUBAIR da HASANUL BASAREE cewa idan ya jinkirta wankan da gangan ba tare da uzuri ba, to azuminsa ya baci.
Amma da ace ba da gangan bane misali da janabar ta kama shi sai yayi barci bai farka ba sai bayan fitowar alfijir to anan Azuminsa ya inganta. Irin wannan hukunci haka yake a ramuwar Azumin watan Ramadan.Amma ga Azumi na nafila ko wadanda ba na watan Ramadan ba ko ramuwarsa to su koda alfijir ya keto yana da janaba da gangan to Azuminsa ya inganta

WALLAHU A'ALAM.

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Post a Comment (0)