FITINANNEN YARO

FITINANNEN YARO

https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURQQ

*TAMBAYA*❓

Mallam ni kuma tambayata yaro ne nayi nayi yayi karatu amma kamar baya dauka sai futuna, Don Allah malam da adduar da zanmasa ko nasamu yayi. Na gode mallam.

*AMSA* 👇

Babu shakka irin wannan matsalar akan sameta dayawa a cikin Al'ummah kuma babban abinda ke kawo wannan matsala duk baifi sakacin uwa bane.
Domin yau zaka iya ganin yara kanana ga lokacin sallah yayi ko lokacin zuwa makaranta yayi amma a kyale yara suna ta kallace-kallacen fina finnai, baza'a umurce su suje makaranta ba ko su tashi suyi sallah ba, ana tunanin ai tunda yaro bai kai shekara tara ba ai bai isa koyon karatu ba ko sallah.
Wanda kuwa ba haka bane, domin MANZON ALLAH (saww) YaCe, "Bakunan ‘ya’yanku su zamanto farkon abinda zai bude da shi kalmar La’ila ha ilLalLah, kuma ku umurce su da fadar La’ila ha ilLalLah lokacin da su ka zo mutuwa"
Shiyasa wasu manazarta sukace, "KA KOYAWA DANKA AL'QUR'ANI YANA 'DAN QARAMI SHI KUMA QUR'ANI ZAI KOYAR DASHI KOMAI NA DAGA DUNIYA"
Ya tabbata a hadisi Cewa, Ummu Sulaym (R.A) tana umurtan danta Anas bin Malik da fadin Lailaha illalLah ta na ce masa, 'dana ka ce La’ilaha illalLah Ashadu anna Muhammadar RasulilLah tana koya masa fadar wannan kalmar ne kafin yaye.
Abinda aka fiso kenan uwa ta rika maimaita kalmar a gaban ‘ya’yanta tun kafin yaye.
amma idan mahaifiya ta kasance tana yawaita zage-zage, ko wasu maganganu wadanda basu dace ba sai yaro ya taso da zage-zage kuma ya taso da fitina.
Haka kuma Zagin yara da tsine masu yana daya da ke jawo wa yara hasara da bala’i a duniya da lahira.
Mafi yawancin ‘ya’ya sukan shiga harkar shaye-shaye da sace-sace da zinace-zinace ne ta sanadiyar tsinuwar da iyayensu suke yi masu tun suna yara kanana.
Wata rana a cikin tawagar MANZON ALLAH (Saww) ana tafiya, sai wata mata ta bugi raquminta ta tsine wa raqumin.
Nan take Sai MANZON ALLAH (saww) Yace, “A tsaya a cire kayan da ke kan raqumin domin mu ba za mu yi tafiya da wanda aka tsine masa ba.”
Yan uwa ku sani Ko da kaza kike da ita a gida kina tsine mata, to idan ta yi qwai sai ta shanye sakamakon tsine mata da kike yi.
Ballantana yaro anfi da so a rika yiwa yara addu'ah akoda yaushe ba tsine musu ba, domin Allah yakan amshi abinda mutum ya kira dansa dashine.
Imamul Bukhari makaho aka haife shi amma saboda addu’ar da mahaifiyar sa take yi kullum tana roqon Allah ya sa idon danta ya bude.
Wata rana tana bacci da dare sai yi mafarkin da Annabi Ibrahim (AS) A cikin mafarkin Annabi Ibrahim ya ce mata in Allah ya so gobe idon 'Danki zai bude.
Da gari ya waye tana zaune da safe tana karatun Qur’ani sai ga Imamul Bukhari ya rugo da gudu yana cewa,MAMA IDONA YA BUDE.
Allah sarki! Wannan ya samu ne sakamakon addu’ar mahaifiyarsa gashi har yau musulunci tana cigaba da amfana da shi.
Don haka yana da matukar muhimmanci a daina tsinewa yara ko da wasa a rika musu addu'a.
Daga cikin addu'o'in da ya dace a rika yiwa yara kuwa.
★ U'IZUKA MIN JAHDIL BALA'I, WA DARAKISH SHAKA'I, WA SUW'IL KADA'I, WA SHAMATATIL A'ADA'I.
Ma'ana:
Ina nema maka tsarin Allah akan wahalhalun bala'i, da kuma riskar wahala, da mummunar kaddara, da dariyar keta daga makiya.
★ ALLAHUMMA IGFENIHEM AS'ALUKAL HUDAH WAS SADAD.
Ma'ana:
Ya Allah ina rokon masa shiriya da dacewa. da dai sauransu.
Allah ya shiryemu mu duka yasa mu dace da rabo.
WALLAHU A'ALAM

Don Allah Yan'uwa Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING, wasu da yawa zasu amfana.

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*

Post a Comment (0)