HUKUNCIN SANYA ZOBEN AZIRFA


HUKUNCIN SANYA ZOBEN AZIRFA 

https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURQQ

*TAMBAYA*❓

Assalamu Alaikum
Tambaya ta itace shin sa zoben Azirfa ya halasta kuwa kuma Annabi (ﷺ) yasa zoben Azirfa Malam.


 *AMSA* 👇

ﻭﻋﻠﻴﻜﻢ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻭﺭﺣﻤﺔ ﺍﻟﻠﻪ.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ،

Sanya zoben Azurfa ya halasta ga Maza da Mata. Sanya zoben zinare ga Mazan wannan al'ummah ta *Annabi Muhammad (ﷺ)* shine haramun qada'an. 

Haka kuma hadisi ingantacce yazo da *Imam Muslim* ya kawo fitaccen littafin sa, hadisi mai lamba 2094, inda yake tabbatar da cewa *Manzon Allah (ﷺ)* ya sanya zoben Azurfa a hannusa na dama.

عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رضي الله عنه: أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لَبِسَ خَاتَمَ فِضَّةٍ فِي يَمِينِهِ فِيهِ فَصٌّ حَبَشِيٌّ كَانَ يَجْعَلُ فَصَّهُ مِمَّا يَلِي كَفَّهُ.
رواه مسلم (2094)

_An karbo daga *Anas bin Malik (radiyallah anhu)* cewa *Manzon Allah (ﷺ)* ya sanya zoben Azurfa a hannun damar sa, a zoben akwai dutsen kasar Habasha, ya sanya shi ne dutsen yana fuskantar tafin hannun sa._

Saboda haka sanya zoben Azurfa ya halasta.

 والله أعلم،

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Post a Comment (0)