TA SANYA MIJINTA YA FARA AUREN HANNU!
*Tambaya*
Assalamu alaikum.
Da fatan Malam yana lafiya. Allah Ya taimaka, Ya kara wa Malam lafiya da imani. Tambaya ce ga Malam.
Menene hukunci matar da bata kula mijinta ta hanyan mu'amalar aure. A sanadiyar rashin samun kulawa daga matar tashi har tayi sanadiyar jefa shi cikin aikata istimna'i? Menene hukuncin su biyu a Musulunci? Allah Ya saka wa Malam da mafificin alkhairi.
*Amsa*
Wa'alaykumussalam
Ya tabbata cikin hadisin bukhari da muslim hadisin Abu-huraura cewa duk matar da mijinta ya kirata shimfidar sa sai taki har mijin ya kwana cikin fushi da ita to mala'iku suna la'antar ta...
Shi kuma ta bangare sa abinda ya aikata ya wuce iyakar da Allah yayi cikin fadar Allah cikin Suratul-Mu'uminoon aya ta 7, yace" Duk wanda suka nemi biyan bukatar su ta wata hanyar da ba saduwar aure ba to wadannan sune suka wuce iya ka ( masu laifi)"
Wadan nan nassoshin biyu na nuna dukkan su sun aikata lafi sai a tuba a nemi gafarar Allah, ita matar ta kara da neman gafarar mijin ta kuma kar ta sake, domin hakan na iya cefa shi cikin hadari kuma yayi sanadiyar halakar sa da ita baki daya bugu da kari aure na iya mutuwa ta sanadiyyar rashin saduwa.
Wallahu A'alam
Malam Nuruddeen Muhammad (Mujaheed)
14/1/2021
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248