HUKUNCE-HUKUNCEN HAILA GA MAI AZUMI 01



*HUKUNCE HUKUNCEN HAILA GA MAI AZUMI* 1️⃣



🔷 Tambaya 1:
Idan mace ta sami tsarki bayan fitowar Alfijir, Shin zata kame baki tayi A
azumin wannan yinin? Ya zamana ta azuminci wannan yinin? ko Kuma ramuwar wannan yinin yana kanta, bayan ta kuma kame bakinta??

🔶 Amsa:- Idan mace ta sami tsarki bayan fitowar Alfijir malamai suna da maganganu guda biyu gameda kame bakinta a wannan yinin;

1️⃣Magana ta farko:- Hakika an dora mata kame baki a ragowar wannan yinin, sai dai shi (Kame bakin) ba za'a kirga mata shiba, wajibine sai ta rama azuminzumin wannan yinin. Wannan shine fitaccen zance a Mazhabar Imamu Ahmad Allah yayi masa rahma.

2️⃣ Magana ta biyu:- Hakika ba'a dora Mata kame bakin ragowar wannan yinin ba, saboda azumi acikin wannan yinin bai halasta ba agareta, kasancewar afarkonsa tana cikin haila, dan haka azumin bai inganta mata ba, kame bakinta bashi da wani fa'ida, wannan lokacin lokacine da bashida wani hurumi agurinta, saboda an umarceta da taci ta Sha acikin farkon ranar, kai barima an haramta mata azumtar sa a farkon Ranar.
Azumi a *Shari'a* shine : 
Kamewa daga ciye ciye da shaye shaye dan bautawa Allah mai girma da buwaya daga fitowar Alfijir har zuwa faduwar rana.
Wannan zance kamar yadda kake ganinsa shine zance mafi inganci daga cewa sai an kame baki,
    Abisa zantukan duka biyu sunyi ittifaƙi akan wajabta mata rama azumin wannan yinin".


📝 المصدر :
[ ٦٠ سؤالا في أحكام الحيض والنفاس/لفضيلة الشيخ محمد بن صالح العثيمين رحمه الله ص٧].

#zaurenfisabilillah
https://t.me/Fisabilillaaah
Post a Comment (0)