*HUKUNCE HUKUNCEN HAILA GA MAI AZUMI* 2️⃣
Tambaya:- Shin idan al'adar mace ya ɗauke sai tayi wanka bayan fitowar alfijir, sai tayi sallah tayi azumi, shin zata rama azumin wannan ranan??
Amsa:- Idan al'ada ya ɗaukewa mace kafin fitowar alfijir koda da minti ɗaya ne kuma hakan a ramadhan ne to ya wajaba akanta tayi azumin wannan ranan, domin tayi azumi tana cikin tsarki, koda kuwa batayi wanka ba sai bayan fitowar alfijir, kamar namiji ne da ya tashi da janaba ajikinsa sawa'un na saduwa ne ko kuma na mafarki, baiyi wanka ba har sai bayan fitowar alfijir azuminsa yana nan babu abinda ya sameshi.
Aƙarƙashin wannan zanso in faɗakar da mata akan wani abu, idan al'ada ta zowa mace bayan faɗuwar rana kafin tayi sallan magriba, azuminta na nan bai ɓaci ba, koda kuwa yazo matane bayan faɗuwar rana da minti ɗaya, azuminta ya cika"
📝 المصدر :
[ ٦٠ سؤالا في أحكام الحيض والنفاس/لفضيلة الشيخ محمد بن صالح العثيمين رحمه الله ص٨].
#Zaurenfisabilillah
https://t.me/Fisabilillaaah