SAURAYINA YANA LUWAƊI, MENENE SHAWARA?



*SAURAYINA YANA LUWADI, MENENE SHAWARA?*

https://chat.whatsapp.com/KeXayNmsBie671pMAKT9xN

*TAMBAYA*❓

ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATULLAH. Malam Barka Da Asuba. 
malam wata 'yar'uwammuce take tambayata tana da saurayi suna soyayya har an sa musu ranar aurensu amma yarinyar sai ta gano saurayin aikinsa neman maza yan uwansa shine take tambayata ta rufa masa asiri suyi aure yahalatta??. Ahuta lafiya bissalam 

*AMSA*👇

Wa alaikum assalam, Ta sanya a yi masa nasiha ko ita ta yi masa, in har ya tuba, tuba ingantacce za su iya yin aure, saboda wanda ya tuba daga zunubi kamar wanda bai taba aikatawa ba ne.

In bai tuba ba ana iya fasa auran saboda mai wannan aikin FASIKI ne, Annabi S.A.W. yana cewa: (Idan wanda kuka yarda da addininsa da dabi'unsa ya zo muku to ku aura masa) kamar yadda Tirmizi ya rawaito.

Mai neman maza dabi'unsa ba yardaddu ba ne, wannan ya sa za'a iya hana shi aure.
Sannan bai kamata a rufa masa asiri ba, musamman idan aka masa nasiha a asirce ya ki tuba saboda Mabarnaci ne.

In har za su yi aure ya kamata ayi gwajin jini saboda yiwuwar ya kwashi wata lalurar ta hanyar masha'ar da ya aikata a baya .
Allah ne mafi sani

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Post a Comment (0)