No title


*AZUMI GARKUWAR MUSULMI* 0️⃣3️⃣
Assalamu alaikum warahmatullah
_______________________
*ABUBUWAN DA SUKE BATA AZUMI*
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
Abubuwan da suke bata azumi,sun kasu kasha biyu
1. Abubuwan da suke bata azumi suke wajabta ramuwa kadai
2. Abubuwan da suke bata azumi sannan suke wajabta kaffara.
      1. wadanda ke wajbta ramuwa kadai gasu kamar haka:
A.Isar wani abu zuwa makoshi [ sakamakon rashin sani] ta hanyar IDO, BAKI, HANCI, KUNNE, DUBURA, AL’AURAR MACE.
B. Zurfafawa a wajen kuskurar baki, zurfafawa ta hanyar shaka ruwa a lokacin alwala
C. Fitar maniyyi ta dalilin sha,awa sakamakon zurfafa tunai, zurfafa kallo, sunbanta [kiss] rungumemeniya, da dai sauransu.
D. Zuwan jinin al’ada [haila], jinin haihuwa [BIKI], RIDDA [fita daga addinin musulunci], Rashin aiwatar da niyyar daukar azumi, kakalo amai da gangan a lokacin azumi.
*TAMBIHI*
Wadannan sune abubuwan da suke wajabta ramuwar azumi, yayin da mutum ya samu kansa acikin halin daya daga cikinsu, to bashi da azumin wannan rana, kuma bayan sallah zai ramashi.
ALLAH SHINE MASANI!
WASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH
Yan uwanku a musulunci
Umar kabir Dakata
Ahmad khamis sani

    
                      *@HAUSA HAZAKA*

FACEBOOK GROUP:-https://facebook.com/groups/710146553060616/

FACEBOOK PAGE:-
https://www.facebook.com/Hausa-hazaka-113088780077744

WHATSAPP:- https://chat.whatsapp.com/J8YnGA8tAAG8eoVirMWzDK

TELEGRAM:-https://t.me/HausaHazaka
Post a Comment (0)