HUKUNCIN AMFANI DA TOZALI, DA KAYAN KWALLIYA A CIKIN YININ RAMADHANA
– Tambaya: Menene hukuncin amfani da tozali ko wasu kayan kwalliya ga mata a cikin yinin ramadhana, kuma shin yana vata azumi ko a’a?
– Amsa: Tozali baya karya azumin ‘ya mace, ko na namiji, a mafi ingancin zance guda biyu na maluma, a kowani irin hali. Saidai kuma ayi amfani da shi da daddare shi ya fi dangane da mai azumi mace ko namiji. Haka kuma abubuwan da mata ke ado da su na sabulu ko mayuka, ko makamancin haka na dangin abubuwan da su ke alaka da fata kawai, misalin su kunshi (lalle), da kayan barbade-barbade da makamantan haka, dukkan wadannan babu laifi ga mai azumi mace, ko namiji su yi amfani da shi, tare da cewa baya halatta a yi amfani da kayan shafe-shafe matukar zai cutar da fiska (kamar canza mata kala). Allah ne majibincin dacewa!