FATAWA AKAN AURE


*``````📌 Albahral Ilmu* 🌴 *```*
*FATAWA A KAN AURE*
===================
 _*HUKUNCIN MACE TA YAFE WA MIJI KWANA A DAKIN TA, SA'ANNAN IDAN TAYI HAKAN ZATA CI GABA DA GIRKI NE?*_ 
===================

 *_Tambaya_* :

Assalam alaikum. Mal. Menene sharudda da hukuncin mayar wa miji kwana daya raba tsakanin matan sa?. Shin zata ci gaba da yin girki ma kan ta ne ita kadai koko har da shi zata yi ta aika mishi na shi 


 *_Amsa_* :

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah.


Bayani ya gabata cewa rabon kwanan aure daban, girki kuma daban, ga mai mata biyu ko abin da ya fi haka.


Don haka ramakon kwana dole ne sai dai idan ita matar ce ta yafe wa mijin domin haƙƙin ta ne.


Amma girki na iya kasancewa tare da ke, ko da yana ɗakin wata. Wannan baya nufin mai kwanan bata da ikon ta bashi abinci, ko ke ki aika mashi da abinci ba, kowace daga cikin ku na iya bashi girki, ya halatta, ko yana ɗakin wata ba naki ba. Dalili shine wani sashe na matan Annabi na aika ma shi da girki alhali yana kwanan wata ba wacce ta aiko girkin ba, kuma bai hana hakan ba, har ma wata rana Nana Zainab ta aika mashi da abinci alhali yana ɗakin Nana Aisha, ma'ana lokacin kwanan ta, sai Nana Aisha ta kaɓar da abincin har ta fasa kwanon, sai Annabi ya ɗauki sabon kwanon ta ya biya Nana Zainab da shi ya kuma ci abincin kuma yayi mata tayi. 
Ga hadisin, riwayar Bukhari 


عَنْ أَنَسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ عِنْدَ بَعْضِ نِسَائِهِ، فَأَرْسَلَتْ إِحْدَى أُمَّهَاتِ الْمُؤْمِنِينَ مَعَ خَادِمٍ بِقَصْعَةٍ فِيهَا طَعَامٌ فَضَرَبَتْ بِيَدِهَا، فَكَسَرَتِ الْقَصْعَةَ، فَضَمَّهَا، وَجَعَلَ فِيهَا الطَّعَامَ وَقَالَ: ((كُلُوا)). وَحَبَسَ الرَّسُولَ وَالْقَصْعَةَ حَتَّى فَرَغُوا، فَدَفَعَ الْقَصْعَةَ الصَّحِيحَةَ وَحَبَسَ الْمَكْسُورَةَ. 


Wannan riwayar Turmuzhiyy ke nan


عَنْ أَنَسٍ قَالَ أَهْدَتْ بَعْضُ أَزْوَاجِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ طَعَامًا فِي قَصْعَةٍ فَضَرَبَتْ عَائِشَةُ الْقَصْعَةَ بِيَدِهَا فَأَلْقَتْ مَا فِيهَا فَقَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: ((طَعَامٌ بِطَعَامٍ وَإِنَاءٌ بِإِنَاءٍ)).







Wallahu ta'aala a'lam.

 *29/10/2020*


 *_Amsawa_* :

 *Malam Aliyu Abubakar Masanawa*


*_Gabatarwa_* 
      *Abdulkadeer Umar Alshinkafawy * 
     
 
 *_Daga_* 
        *Zauren*
*📌Albahral Ilmu 🌴*
 Ga masu son shiga tura sunan ka/ki da number ta WhatsApp.
     *07064746551*
Post a Comment (0)