HUKUNCIN FAMILY PLANNING



HUKUNCIN FAMILY PLANNING 

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds

*TAMBAYA*❓

Shin yahalatta Mace tayi Family Planning idan Mijinta bayason yawan 'Ya'ya saboda tsoron daukan nauyinsu??
:

*AMSA*👇

:
Abinda Malamai sukace agameda irin wannan Mas'Ala shine, farkodai babban abinda yakamata asani shine Asali Ma'aurata dukkansu kowa yanada haƙƙi akan Ɗan'uwansa agameda abinda yashafi 'Ya'yansu dakuma Ɗaukan ciki, shiyasama a Shari'ance akace kada Miji yayiwa Matarsa AZALU (yafitar da maniyyinsa ba'acikin farji ba) dole sai idan yanemi izininta kuma tayarda, to hakanan itama Mace bazatayi abinda zata hanawa kanta ɗaukar cikiba batareda sanin Mijintaba dakuma izininsa, to idan hakane ashe kenan baya halatta ga Mace tasha Maganin da zai hanataɗaukar ciki batareda izinin Mijiba, ƘIYASI kenan akan cewa shima Miji bai halattaba yayi Mata AZALU ba saida izininta, wannan fa ana magane akan Mata masu Uzuri da Shari'a tabasu izinin cewa zasu iyayin tazarar Haihuwa, amma Shan magani da nufin hana haihuwa gabaɗaya dan gudun kada sutara 'Ya'ya dayawa, to wannan kam babu wani Saɓani akancewa Haramunne (Ƙaulan-Wahidan) Saidai duk dahaka Malamai sukace idan akasamu wani UZURI mai ƙarfi, kamar yakasance ace Mace zata'iya samun cutuwa maitsanani adalilin daukan cikin, tareda shaidar amintattun Likitoci da sukace hakan, to a'irin wannan hali ya halatta tasha maganin hana ɗaukan ciki koda kuwa Mijin bai saniba, domin anan haƙƙin Mijin ya saraya saboda dole afara gabatarda Maslahar ita Matar gameda lafiyarta akan haƙƙin da shi Mijin yake dashi akanta, wannan kuma dama ƘA'IDACE TA USUL, kuma Mαɳzσɳ Aʅʅαԋ( ﷺ ) yace:
:
" ﻻ ﺿﺮﺭ ﻭﻻ ﺿﺮﺍﺭ "
‏( ﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﻪ )
MA'ANA:
Babu cuta Babu cutarwa:
:
Sannan Kamar yadda Malamai sukace ya halatta azubarda ciki kafin ahura masa rai idan yakasance ansamu bayani daga wajen Ƙwararrun Masana kiwon Lafiya cewa lallai idan ba'azubar da wannan cikinba to akwai tabbas ɗin cutuwa agameda lafiyar ita Matar, to anan babu laifi azubar da cikin domin aceto rayuwar ita Matar,
:
Amma haka kawai bai halatta Mace tayi amfani da maganin hana ɗaukan cikiba kawai dan saboda kasancewar Mijinta yanada wata mummunar Ɗabi'a ko dan saboda bayason yatara 'Ya'ya dayawa, kokuma saboda Miji baya saukewa Mace haƙƙinta yadda yakamataba, to dukkan wadannan abubuwa da makaman tansu bazasu zama Hujja ko Dalili na Mace ta hanawa kanta ɗaukan cikiba, kokuma tace zata hana masa kanta yasadu da'ita,
:
Hakanan baya halatta Miji ya tursasawa Matarsa cewa dole sai tadena haihuwa, wai dan saboda jin tsoron tarbiyyar 'Ya'yan kokuma Ɗaukan nauyinsu, domin yin hakan munana zatone ga Aℓℓαн( ﷻ ), domin kuwa dukkan wata halitta da Aℓℓαн( ﷻ ) zeyi to dama ya tanadar mata da daidai gwargwadon arzikinta, kamar yadda Yake cewa:
:
" ﻧﺤﻦ ﻧﺮﺯﻗﻬﻢ ﻭﺇﻳﺎﻛﻢ، " ‏( ﺍﻹﺳﺮﺍﺀ 31/ )
MA'ANA:
Mune muke azurtasu ('ya'yan da'aka haifa) dakuma ku kanku (iyayen),
:
Danhaka baya halatta ga Ma'aurata su tsayar da haihuwa gabadayanta kawai dan saboda tsoron talauci, domin tara Dukiya maiyawa dakuma tara 'Ya'ya masu yawa hakan yana daga cikin kayan ado na rayuwar Duniya, kamar yadda Aℓℓαн( ﷻ ) Yafaɗa, amma abin Mamaki yau sai akawayi gari Mutane suna iyaƘoshi da yawan 'Ya'ya amma basa Ƙoshi da yawan dukiya, kuma dayawa Aℓℓαн( ﷻ ) yakan ɗaga darajar wasu Mutanene a sakamakon yawan 'Ya'yansu:
( ﻭَﺍﻟـﻠَّـﻪُ ﺳُـﺒْـﺤَـﺎﻧَـﻪُ = ﻭَﺗـَﻌَــﺎﻟـَﻲٰ ﺃَﻋْـﻠَـﻢُ )
:
Doмυn nЄMan Ƙarin bayani sai aduba waɗannan Լitattafai kaMar Ӈaka:
↓↓↓
:
" ﺍﻟﻤﻮﺳﻮﻋﺔ ﺍﻟﻔﻘﻬﻴﺔ " ‏( 3/156 ‏)
:
ﺍﻹﻧﺼﺎﻑ ‏( 1/272 ‏)
:
ﻛﺸﺎﻑ ﺍﻟﻘﻨﺎﻉ ‏( 2/96 )

Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING, wasu da yawa zasu amfana.

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)