HUKUNCIN MATAR DA TAKE DAUKAR KUDIN MIJINTA BAI SANI BA?



HUKUNCIN MATAR DA TAKE DAUKAR KUDIN MIJINTA BAI SANI BA?

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum malam, meye hukuncin matar da take daukar ma mijinta kudi bai sani, ko wani abu nashi ba tare da ya sani ba ta yi bukatunta da su? Wassalam.


*AMSA*👇

Wa'alaikumus salam, matar da take ɗaukar kuɗin mijinta ta yi amfani da su saboda mijinta maqeqe ne ko mai qoro, ba ya ba su abincin da zai ishe su, to ya halasta ta teɓi kuɗinsa su ci abinci gwargwadon buqatarsu ba tare da ɓarna da almubazzaranci da dukiyar ba, dalili a kan haka shi ne:
Nana A'isha Allah ya qara mata yarda ta ruwaito hadisi cewa: Lallai Hindu Æ´ar Utbata ta ce: Ya Manzon Allah lallai Abu Sufyana ya kasance mutum ne maqeqe, ba ya ba ni abin da zai ishe ni da Æ´aÆ´ana, face sai abin da na É—auka daga wurinsa bai sani ba, sai Manzon Allah ï·º ya ce: "Ki É—auki abin da zai ishe ki da Æ´aÆ´anki tare da kyautatawa". Bukhariy 5364.
Wannan hukuncin ya keɓanta ne kaɗai ga matar da mijinta ba ya ciyar da su yadda ya dace saboda maqo alhali yana da hali. Amma duk matar da mijinta ke ba su haqqoqin ciyarwa gwargwadon hali, to idan ta ɗebi kuɗin mijinta bai sani ba ta yi amfani da su, tabbas ta ci haramun, sai ta biya shi gobe Alqiyama, kuma abin da ta yi sunansa ha'inci, ko zamba cikin aminci.
Amma raguwar abinci ko raguwar abinsha da a al'adance mace kan yi sadaka da shi ga baqi ko makamantansu wannan babu laifi don mace ta bayar da su sadaka. Amma rumbun abincinsa bai halasta ta É—ebo ta yi sadaka da shi ba sai da saninsa.
Allah S.W.T ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*

Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING, wasu da yawa zasu amfana.

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Post a Comment (0)