HUKUNCIN SHAN RUBUTU A MUSULUNCI



HUKUNCIN SHAN RUBUTU A MUSULUNCI 

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds

 *TAMBAYA* ❓

Aslm malam barkada yamma dan allah malam menene matsayin shan rubutu a musulunci

 *AMSA* 👇

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Babu laifi rubuta wasu ayoyi na Alqur'ani acikin Allo ko takarda da ruwa mai tsarki ko tawada ko wani abu da baya cutarwa mai tsarki kamar za'afaran da Ma'u wardi awanke asha ko ashafa ruwan a inda ciwo yake ajikin mutum, saboda ruwaito haka da'akayi daka Malaman Salaf magabata Na kwarai.
Ibnul qayyeem Allah yajikansa acikin zhadul ma'adi (4/170) yace: dangane da ruqyar kambun baka, " Wasu jam'a daka cikin Salaf suna ganin babu laifi arubuta wasu ayoyin Alqur'ani sannan mutum yasha, Mujahid yace: Babu laifi arubuta wasu ayoyin Alqur'ani awanke abaiwa mara lafiya yasha, an ruwaito irin wannan daka Abu qilaba daka Ibnu Abbas Allah yaqara musu yarda: Ya Umarci arubutawa wata mace wasu ayoyi na Alqur'ani saboda wahalar da dan dake cikinta yake bata, sannan aka wanke mata aka bata tasha, Ayyub yace: Naga Aba qilaba yarubuta wani rubutu na Alqur'ani sannan yawankeshi da Ruwa yabaiwa wani mutum da bashi da lafiya yasha.
Yazo acikin Fatawa lajnatul da'imah (1/97) " Karanta Alqur'ani ko Sunnah ga mara lafiya ana tofa masa ya tabbata asunnah ingantacciya daka ruqyar manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam wacce yayi dakansa dakuma Wasu daka cikin Sahabbansa, rubuta alqur'ani da Ma'u wardi ko za'afaran damaka mantansu sannan asanya aruwa asha, ko karanta qur'ani acikin Zuma ko nono da makamantan haka da turara jiki ko shafe jiki da Al-miski da ma'u wardi wanda aka karanta ayoyin alqur'ani acikinsa babu laifi, Magabata na kwarai sunyi haka.
Shaik Bin Baaz rahimahullahu yace: rubuta Alqur'ani da Addu'o'i ingantattu da za'afaran ajikin Allo ko wani mai tsafta ko takarda mai tsafta sannan a wankewa mara lafiya yasha babu laifi akai, dayawa daka cikin magabata Sun aikata haka, kamar yanda ibnu qayyeem ya fadada bayani da waninsa acikin zhadul ma'adi, idan wanda zai hakan yana cikin wadanda aka shaidesu da Alkhairi dakuma Tsayuwa akan dokokin Allah.
Fatawa Islamiyyah (1/30).
Tanbihi: Wannan yashafi rubutu daza'ayi dan ruqya ko wata cuta.
Amma irin rubutu da Alarammomi sukeyi arubuta ya Allahu qafa dubu ko yasin sau hamsin ko ya ladifu kafa dari, ko a gutsuro wata kalma daka wata aya adakko daka wata ahada arubuta cikin Allo ko sau wani adadi, Wannan bai halatta ba.
Hakama wani Alaramma yamaida kansa koda yaushe aikinsa yayi rubutun sha abiyashi ko abashi sadaka aikinsa kenan din-din wannan baida Asali acikin shari'ar musulunci.
Allah madaukakin Sarki yadatar damu baki daya.
Wallahu A'alamu.

Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING, wasu da yawa zasu amfana.

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)