SHIN AKWAI WATA ADDUA TA MUSAMMAN TA SHIGA WATAN RAMADHANA????:
Mafi yawan mutane suna tambaya akan ko akwai adduar da ta tabbata daga Manzon Allah ﷺ yana fada dan shiga watan Ramadhana??
Wasu kuma suna turawa mutane da wasu addu’oi akan sune adduar shiga watan Ramadhana shin wannan addu’oin sun inganta??
An tambayi daya daga cikin Manyan Malaman duniya na ahlussuna na yanzu wato;
الـعَلّامـَةصَالِح بنُ فَـوْزَان الفَـوْزَان -حَـفِظَهُ الله – :
Tambaya;
*”Shi akwai wasu addu’o’i na musamman da ake karantawa lokacin shiga watan Ramadhana?? Kuma wani abune ya zama wajibi akan musulmi yayi addua da shi lokacin da shiga wannan wata mai albarka???*
AMSA
*”Ban san wani addua ba ingantacciya ba da aka kebeta ba dan shiga wannan wata mai albarka ba,sai dai akwai addua gamammiya da ake karantawa lokacin da aka ga sabon jinjirin wata,wannan kuwa ana karantawane a kowane wata na shekara ba watan Ramadhana ba shi kadai”*.
Domin Manzon Allah ﷺ ya kasance idan yaga sabon watan Ramadhana ko wani watan wanda ba Ramadhana ba yana cewa:
*(اللَّهُمَّ أَهِلَّهُ عَلَيْنَا بِالْيُمْنِ وَالإِيمَانِ، وَالسَّلامَةِ وَالإِسْلامِ، هِلَالُ خَيْرٍ وَرُشْدٍ، رَبِّي وَرَبُّكَ اللَّهُ)*
Awani sahe na wata Riwayar yana cewa:
*(اللهُ أَكْبَر، اللَّهُمَّ أَهِلَّهُ عَلَيْنَا بِالأَمْنِ وَالإِيمَانِ، وَالسَّلامَةِ وَالإِسْلامِ، رَبِّي وَرَبُّكَ اللَّهُ)*
Wannan itace adduar da ta tabbata a sunnar Manzon Allah ﷺ da ake karantawa lokacin ganin sabon watan Ramadhana sauran watannin shekara gaba daya.
Amma ware shiga watan Ramadhana da wata addua ta musamman ba wannan da Annabi ﷺ ba,ban san wani abu da ya tabbata a sunna ba yin hakan.
Amma babu laifi idan mutum ya roki Allah lokacin shiga wannan wata da adduar irin sigar adduar da yaga dama,amma ware wata siga ta musamman ga jama’a baki daya,to wannan bai tabbata a Sunnar Manzon Allh ﷺ ba.
Allah ne mafi sani.