HUKUNCIN MACE MAI HAILA TA KARANTA ƘUR'ANI TA WAYA


*HUKUNCIN MACE MAI HAILA TA KARANTA ALKUR'ANI A WAYA📱*

https://chat.whatsapp.com/LRPQDrs7qSoKXuSspoPkFm

*TAMBAYA*❓

MENENE HUKUNCIN KARATUN ALQUR'ANI ACIKIN WAYA, IRIN APPILICATION DINNAN UZU SITTIN, YAYA HUKUNCIN MACEN DA BATA DA TSARKI TADAU WAYAR TAI KARATU ACIKI.

*AMSA*👇

Alqur'anin Application Nawaya rubutacce wanda ake karantawa, kona sauti wanda ake saurara baya daukar hukinci alqur'ani cikakke wanda ke rubuce acikin takardu. ya hallata tabashi acikin wayar ko karantashi batare da tsarki ba, kuma ya halatta shiga bandaki dawayar, saboda rubutun alqur'anin dake cikin waya bakamar rubutunsa bane dake cikin takardu, Kawai wasu na'urorine suke bijirowa sannan saisu gushe, ba haruffa bane tabbatattu, waya kuma tahada Qur'anin dawasu abubuwan.

An tambayi shaik Abdurrahman bin Nasir menene hukuncin karanta alqur,ani na cikin waya batare da tsarki ba?

Saiya Amsa: Abune sananne karatun alqur'ani wanda mutum yahaddace basharadi bane sai mutum yana da tsarkin kari karami harma da babban kari, Saidai karanta alqur'ani tare da tsarki koda tilawa mutum zaiyi karatun shine yafi, domin zancen Allah ne, yana daka cikin girmama zancen Allah kada akaranta sai anada tsarki.

Amma karantashi acikin takardu sharadine kai tsaye sai idan mutum yanada tsarki, Saboda Abunda yazo acikin hadisi shahararre ( Baya halatta adauki alqur'ani ko shafarsa sai wanda yake da tsarki) Dakuma abunda yazo na maganganun sahabbai dakuma tabi'ai, Akan haka jamhurdin malamai suka tafi akai, Shine wanda yake da hadasi haramunne ya taba alqur'ani saboda tilawa kowanin tilawa.

Abisa wannan zai bayyana garemu cewa Alqur'anin dake cikin waya dasauran na'urori wanda ake taskance abubuwa acikinsu baya daukar hukuncin Alqur'anin dake rubuce acikin takardu, domin rubutunsa yasaba dawanda yake acikin takardu, bazaka samesu da siffofinsu da'ake karanta suba, saidai asamesu asifar yanada na'urar kebayarda haruffan yayinda aka nema, saita bayyanar dashi ascreen idan kuma ka tsallaka kan wani abun acikin wayar sai haruffan su kau, Abisa wannan yahalatta daukar wayar ko shafarta, ko wani kaset da'aka taskance Alqur'ani acikinsa, ya halatta karantashi, koda mutum baida tsarki.

Shaik Salih Alfauzan yace: Alqur'anin dake rubuce acikin takardu Bai hallata shafarsa ko taba shi ba saiga wanda yakeda tsarki kamar yanda yazo acikin hadisi, Amma waya ba'a kiranta Alqur'ani.

Karanta Alqur'ani acikin waya saukakawane ga mai haila, da kuma wanda daukar alqur'anin gaba daya yake masa wahala, ko yake wajan dazai masa wahala yin alwala, saboda rashin tsarki.

Saboda haka ya halatta macen da bata da tsarki ta karanta alqur'ani na appilication, ba haramun bane danta dauki wayar kotayi karatu dashi lokacin dabatada tsarki.

 Wallahu A'alamu

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: 👇_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)