HUKUNCIN MAI WASA DA GABANSA


*HUKUNCIN MAI WASA DA GABANSA* 

https://chat.whatsapp.com/IZhc4HXjGXFDOuOmx3ceZA

*TAMBAYA*❓

Malam meye hukuncin Mai wasa da gabansa harsai yasamu biyan bukatarsa

*AMSA*👇

Yin haka bai halatta ba. Kuma yana daga cikin MANYAN LAIFUKA A MUSULUNCI.
Yana janyowa mai yin hakan FUSHI DA KUMA TSINUNWA DAGA UBANGIJI (SWT).
Manzon Allah (saw) yana cewa:
"MUTUM BAKWAI, ALLAH YATSINE MUSU. KUMA BA ZAI DUBE SU DA RAHAMA BA ARANAR ALQIYAMAH. KUMA ZAI CE MUSU: "ku shiga wuta tare da masu shigarta".
1. WANDA YAKE YIN LUWA'DI.
2. WANDA AKE YIN LUWA'DIN DASHI.
3. MAI YIN ZINA DA DABBOBI.
4., 5, 6, MAI YIN ZINA DA UWA, SANNAN KUMA YAYI DA 'YARTA.
7. MAI YIN ZINA DA HANNAYENSA (mai yin wasa da azzakarinsa
da kuma Mace Mai yin Hakan ga al'aurarta).
Sannan Kuma Shi irin wannan Aikin yana daga cikin irin Laifukan da Mutanen Annabi Lut (as) Suke yi.
* An Ruwaito cewar Duk masu yin haka idan basu tuba ba, ZASU TASHI ARANAR ALQIYAMA HANNAYANSU SUN DAUKI CIKI (juna biyu).

* Likitoci MaSu ilimin Sanin Lafiyar jikin Bil-Adama sun fadi wasu Illoli da dama wadanda yin hakan yake haifarwa:
1. MANTUWA MAI TSANANI. (mantuwar karatu, etc).
2. RAUNIN IDANU: masu yinhakan idan basu dena ba, sukan makance kafin wani lokaci mai nisa.
3. RAUNIN AL'AURA: Duk masu yin haka, idan suka yiaure, Sukan yi fama da rashin karfin Azzakari, saboda duk Maniyyin da aka fitar dashi da-gan-gan, Ba ya fita gaba-daya.
Wannan wanda ya saura, Sai ya daskare Maka acikin Mararka.
4. RASHIN HAIHUWA: Wannan daskararren Maniyyin, yana kashe kwayoyin halitta daga jikinNamiji ko mace..
5. CIWON HAUKA: da kuma Kaskanci.
Wannan dan kadan na Tsakuro daga cikin Irin illolin da wannan Al'amari yake haifarwa Ajikin Mata da Maza.
Da fatan Allah ya shiryi DukMasu yi su dena.

Wannan al'ada itace malamai suke kira istimna'i wato mutum yaiwasa da gabansa har maniyyi yafita mace ko namiji.
Wanda haramunne a alqur'ani da hadisi
Ibnu kaseer rahimahullah yace : Imamu shafi'i da wadanda suka goyi bayansa yakafa hujja da haramcin wasa da gaba da fadin Allah madaukakin sarki.
( ﻭﺍﻟﺬﻳﻦ ﻫﻢ ﻟﻔﺮﻭﺟﻬﻢ ﺣﺎﻓﻈﻮﻥ ﺇﻻ ﻋﻠﻰ ﺃﺯﻭﺍﺟﻬﻢ ﺃﻭ ﻣﺎ ﻣﻠﻜﺖ ﺃﻳﻤﺎﻧﻬﻢ ﻓﺈﻧﻬﻢ ﻏﻴﺮ ﻣﻠﻮﻣﻴﻦ ﻓﻤﻦ ﺍﺑﺘﻐﻰ ﻭﺭﺁﺀ ﺫﻟﻚ ﻓﺄﻭﻟﺌﻚ ﻫﻢ ﺍﻟﻌﺎﺩﻭﻥ .
Muminai sune wadanda dangane dafarjinsu suke kiyayeshi, sai ga matayensu ko kuyanginsu dan basu kiyaye farjinsu akansu ba, su ba'ababen zargi bane, duk wanda yanemi wata hanya bata aure ba kota kuyangarsa wannan mai ketara dokokin Allah ne.
Imamu shafi'i acikin littafin Aure yace saiya kasance Allah yabayyana kiyaye farjinsu saifa akan matayensu ko abinda damarsu tamallaka, sai yazama haramun idan ba matar ka bace ko kuyangarka sai Allah ya karfafi maganar dacewa " wanda ya nemi koma bayan hakan yana cikin masu taka dokokin Allah"
Bai halatta amfani da azzakari ba sai akan matarka baiwarka, bai halatta jindadi dashi da hannu ba wallahu A'alamu kitabul ummu na imamu shafi'i.
Wasu malaman sun kafa hujja taharamcin istimna'i da fadin Allah madaukakin sarki
( ﻭﻟﻴﺴﺘﻌﻔﻒ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻻ ﻳﺠﺪﻭﻥ ﻧﻜﺎﺣﺎ ﺣﺘﻰ ﻳﻐﻨﻴﻬﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﻦ ﻓﻀﻠﻪ ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﻨﻮﺭ 33
Wadanda basu samu damar aure ba sukame harsai Allah ya wadata su daka falalarsa.
Sukace: umarni da kamewa yana nuna hakuri da rashin samun yin auren ko kuyangar.
A sunnah kuwa sunkafa hujja da hadisin Abdullahi dan mas'ud Yardar Allah takara tabbata agareshi yace: Munkasance tare da Annabi sallallahu Alaihi wasallam muna samari bamu samu komai ba sai Annabi sallallahu Alaihi wasallam yace damu "ya ku taran samari duk wanda yasamu halin daukar dawainiyar iyali yayi aure, domin ya nasa kamewa daka gani, yana kuma tsare farji, wanda kuma bai samu dama ba to nahore shi dayin azumi domin azumi yana kariya daka fadawa haram. Bukhari 5066.
Sai shari'a ta shiryar lokacin da mutum yagajiya wajen yin aure saiya dunga azumi tare da wahalarsa, shari'a bata shiryar zuwa wasa da farji ba, tare da saukinsa akan azumi tare dahaka ba'a halatta shiba.

 *MAGANI GA WANDA YAFADA CIKIN WANNAN DABI'A SUNE KAMAR HAKA* 

1-Wajibine mutum yakubutar dakansa daka wannan al'ada dan nisantar abunda Allah ya haramta da kwatanta bin umarninsa da gujewa fushin sa.
2-kawar da wannan da lafiyar jiki shine aure saboda wasiyyar manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam ga samari.
3-Kawar da hadurra da waswasi da zuciya zata dunga sakawa, da shagalta datunani cikin abunda zai amfaneka duniya da lahira, domin yawan waswasi datunani yanakai mutum zuwa ga aikata abu, sannan mutum yasaba tayanda zai masa wahalar gasken gaske wajen kubuta daka aikata shi .
4-Kamewa daka gane gane domin kallace kallacen wasu abubuwa da hotuna nazane damasu motsi rayayyu ko matattu yana kai mutum zuwa haram.
5-Shagaltuwa da ibadoji kala kala dakin barin sarari ga aikin sabo.
6-Izna da cutukan dake haifarwa jiki na raunin gani da gabbai da ciwan baya da sauransu.
7-Riko da maganin manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam shine azumi.
8-Lazimtar ladubban shari'a yayin bacci na karanta zikirori
9-Kaskantar dakai ga Allah daneman taimakonsa.
10-Gaggauta tuba da istigfari da aikata ayyuka na gari, tare da rashin debe tsammani daka Allah.
11-Kanisanci kwana kai kadai adaki domin Annabi sallallahu Alaihi wasallam yahana mutum yakwana adaki shi kadai.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪ ﻙ ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻧﺖ ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ .

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)