MAI YAWAN WASI-WASI A CIKIN SALLAR SA


*MAI YAWAN WASI-WASI ACIKIN SALLARSA !!* 

https://chat.whatsapp.com/IZhc4HXjGXFDOuOmx3ceZA

*TAMBAYA*❓

slm mlm anwuni lfy 

mlm ina yawan kokwanto a cikin sallah ta kuma wlh sai nazo tsakiyar sallah

allah ya sakawa mlm da alkairi

*AMSA*👇

Was-wasi acikin Sallah kala biyu ne.
1. Akwai wanda yake faruwa ta dalilin sakaci da shagaltuwa da sha'anin duniya da kuma rashin damuwa da Sallar daga wajen Shi MAI SALLAR.
Ta yadda zaka ga mutum yana sallah amma idonsa akan hanya, ko ta window yana ganin masu wucewa.
Ko kuma mutum yana Sallah amma ya kunna T.V. agabansa ko radio. (ba yaso labarai su wuceshi).
Ko kuma kaga Alhaji yana Sallah a Masallaci amma zuciyarsa tana kasuwa. Harma wasu lokutan idan Liman yayi rafkanuwa aSallar, da zarar Mamu sunyi Kabbara sai kaga Alhaji ya firgita. Azatonsa ko YAQI aka soma.
Hukuncin irin wadannan Was-Wasin, Haramun ne. idan ma basu 'batawa Mutum Sallarsa ba, to zasu iya kaishi izuwa Rasa ladan sallar.
2. Was-wasi na biyu kuma Shine irin was-wasin da Shaitanun Aljanu suke haifarwaMutum idan sun shiga jikinsa, ko kuma su na son su shiga.
Zaka ga masu fama da irin wannan larurar suna da yawan kokwanto acikin yawancin lamura. Musamman ma asha'anin Ibada.
Zaka ga idan sunzo Sallah su na yin iyakar bakin Kokarinsu wajen Kiyayewa, amma inaa! Zaka ga sun kidime sun rikice sun manta ko raka'a nawa sukayi.
Galibi ma tunane-Tunane irin na Sa'bon Allah ne zasu rika zuwa musu acikin Sallar.
Irin wannan babu laifi akan shi Mai sallan. Domin kuwa yana yin iyakar kokarinsa. Wani ma har kuka zaka ga yana yi.
Kuma abin ya riga ya zama masa chuta ko larura.
Maganinsa Shine:
° Mutum ya dage da yawan ambaton Allah acikin dukkan motsinsa. Duk abinda zaiyi ya fara da Basmalah.
°° Yawaita karatun Alqur'ani. Da kuma sauraron sautin Alqur'ani.
°°° Ya rika karanta Azkar na safe da yamma. Da na kwanciyar bacci da tashi.
°°° Ya dena barin najasa tana dadewa ajikinsa. Ya yawaita zama cikin tsarki da alwala.
°°° Ya gujewa ayyukan sa'bo manya da kanana.
°°° Duk lokacin da zaiyi Sallar ya rika karanta Du'a'ul-Istifta hi Afarkon Sallar.
insha Allahu zai samu saukin abin.
Malamai sunce duk wanda irin wannan kokonton ya aureshi, yayi sujjadah ba'adi (duk sanda ya idar daSallar).

WALLAHU A'ALAM.

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Post a Comment (0)