MU YAWAITA SALLAR NAFILA

*MU YAWAITA SALLAR NAFILA*

Yawan Sallar Nafila yana sanyawa bawa ya sami daukaka a aljanna kuma Allah ya gafarta masa kurakuransa.

Sallar Nafila tana da falala mai yawa:

-Tana cike gurbin abinda yarage na Sallar farillah agobe Alkiyama.

-Tana sanyawa mutum ya sami makwabtaka da Annabi SAW

-Tana sanyawa bawa ya samu Daukaka awajan Allah.

-Tana sanyawa bawa ya samu dauka agidan aljanna.

-Tana sanyawa bawa ya sami kankarar zunubansa awajan Allah.

Annabi SAW yana cewa:
*"Ku yawaita yin Sujada(sallar nafila),domin babu wani musulmi wanda zai Sujada ga Allah madaukakin sarki face:Allah ya daukaka darajarsa a aljanna.Kuma ya kankare masa zunubansa saboda da wannan sujadar"*
@ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﺔ ١٥١٩
Allah ka bamu ikon yawaita aiyukan nafila.

Post a Comment (0)