HUKUNCIN MATAR DA TAYI ZINA KAFIN AURE
https://chat.whatsapp.com/IQUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E
*TAMBAYA*❓
Assalamu alaikum ya kokari Malam.
Idan mutum yayi zina lokacin baiyi aure ba, yanzu sai yaji wa'azi zai mika kanshi ne ayi masa hukunci bisa shari'ar musulunci? Ko kuwa yaya zai yi?
Na ta'ba tambayar wani Malami sai yace wai koda mutum ya tuba Allah bazai karba ba, kuma lallai sai mutum yayi wani irin mummunan wari alahira kamar yadda dukkan mazinata keyi. Kuma yace babu ruwan wanke wannan warin sai an dulmiya mutum acikin wutar jahannama.
Malam hankalina ya tashi na rasa yadda zanyi.
Ko kuwa in gaya wa mijina?? Don Allah ka taimakeni da fatawa da shawara.
Nagode.
*AMSA*👇
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Hakika tabbas zina babban laifi ne wanda in banda shirka babu laifin da ya fishi girma.. Kuma koda mace tana da aure ko bata dashi, idan tayi zina tabbas ta sabawa Allah, kuma taci amanar kanta, taci amanar iyayenta da danginta, kuma taci amanar mijin da zai aureta, harma zuriyar da zata haifa nan gaba.
Kuma in har ta mutu bata tuba ba, Allah yana iya yafe mata, ko kuma ya azabtar da ita da irin azabar da yayi tanadinta ga mazinata.
To amma abinda yafi daidai da fahimtar Mazhabobin Ahlus Sunnah wal Jama'ah shine duk wanda ya tuba daga zunubi kuma yayi nadama sannan ya nisanci wannan laifin, to Allah zai gafarta masa wannan laifin koda kuwa yayi shekaru masu yawa yana aikatawa..
Allah ya fa'da acikin Alqur'ani cewa:
*"SAI DAI WADANDA SUKA TUBA BAYAN HAKA KUMA SUKA KYAUTATA (AYYUKANSU) TO HAKIKA ALLAH MAI GAFARA NE MAI JIN QAI"*
Kuma duk girman laifin mutum in dai ya tuba da gaskiya, to Allah zai karbi tubansa ya gafarta masa kamar yadda ya umurci Annabi ï·º ya gaya mana :
*"KACE YAKU BAYINA WADANDA SUKA AIKATA BARNA BISA KANSU!! KAR KU FIDDA TSAMMANI DAGA (SAMUN) RAHAMAR ALLAH. HAKIKA ALLAH YANA YAFE DUKKAN ZUNUBAI BAKI DAYA, HAKIKA SHI SHINE MAI GAFARA MAI JIN QAI"*
Ba'a shiga tsakanin Allah da bawansa. Babu wani mai ikon yiwa bawa azaba ko gafara in banda Allah. Kuma idan Allah yaso ya yafe wa bawansa babu wanda ya isa ya hanashi.
Ya kamata malamai su zama masu kiran mutane ne zuwa ga Allah, ta hanyar nuna musu hanyoyin samun kusanci daShi, ba wai su rika kore bayin Allah ta hanyar tsoratarwar da babu albishir acikinta ba.
Shi kuwa maigidanki, kada ki sanar dashi komai acikin wannan, tunda Allah ya rufa miki asiri ya suturceki, kada ki yaye suturar da Allah ya lulluba miki. Yin hakan zai janyo zubewar Qimarki da mutuncinki agun mijinki, kuma bazai Qara yarda dake ba.
Manzon Allah ï·º yace:
*"KU NISANCI WADANNAN QAZANTAR DA ALLAH YA HANA, WANDA KUWA YA SHAFU DA ITA, (WATO YA AIKATA) TO YA LULLUBU DA SUTURAR NAN TA ALLAH, KUMA YA TUBA ZUWA GA ALLAH...."*
Imamul Hakim ne da Malik suka ruwaitoshi.
WALLAHU A'ALAM.
Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
*_Group Admin: 👇_*
*MAL. HAMISU IBN YUSUF*