HUKUNCIN SADUWA DA AMARYA RANAR DA BA GIRKINTA BA
https://chat.whatsapp.com/IQUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E
*TAMBAYA*❓
malam mubiyune wajen mijin mu malam koba ranan girkinaba seyashigo yayi sex Dani Kuma wani lokaci dagangan yakeyi dun waccen taji haushi namai magana yace yasan meyakeyi malam me ne ne hukuncin hakan
*AMSA*👇
Tom abinda zakiyi shine ki nuna masa 'kin abinda yake yi kuma kiyi masa nasiha cikin ladabi da girmamawa cewa: abinda yake yi ya sabawa shari'a kuma akwai zunubi ga aikata hakan. domin kuwa duk me cutar da matarsa a tsakaninta da kishiyarta ma'ana fifita daya daga cikinsu cikin hakkin da sukayi tarayya da juna to ranar alkiyama zai tashi yana mai shanye da barin jiki kamar yadda nassin hadisi ya nuna.
.
_Idan yaki ji sai ki 'ki amince masa idan ya nemeki a irin lokacin koda yayi fushi dake bazaki shiga cikin jerin matan da Allah da mala'iku suke la'antar su ba Matukar dai ita abokiyar zaman naki tana gari ba ita ta bashi izini ba kuma ba wani uzurin Shari'a ne ya hana ya kusanceta ba to be halatta ki amince masaba._
.
_Amma idan akwai uzurinda zai hana ya kusanceta koda a ranar kwananta ne misali kamar tana haila ko jinin haihuwa ko bata da lafiya d.s.s. To wannan babu laifi idan ya bukaceki a irin lokacin kamar yadda kema zaki iya samun kanki cikin ire iren wandannan uzurirrikan da zasu hana ya kusanceki koda kuwa a ranar girkinkine_
..
Wallahu A'alam
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ
*ALLAH TA'ALA YASA MUDACE*
Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
*_Group Admin: 👇_*
*MAL. HAMISU IBN YUSUF*