HUKUNCIN MUTUMIN DA YA BAR AZUMI HAR WATA SHEKARA BE BIYA BA


*HUKUNCIN MUTUMIN DA YABAR AZUMI HAR WATA SHEKARA BAI BIYABA* 

https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf

MENENE HUKUNCIN WANDA AKE BINSA AZUMI HAR WANI AZUMIN YAZO BAI RAMA BA YAYA ZAIYI?
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺍﻟﻌﻔﻮ ﺍﻟﻐﻔﺰﺭ .


*AMSA*👇

Malamai sunyi ittifaqi akan wajabine akan wanda yasha azumi acikin ramazhana yai gaggawar ramawa kafin wani ramazhan din yazo,
Sun kafa hujja da Abunda *Bukhari yaruwaito (1950) da Muslim ( 1146)* daka Aisha Allah yakara yarda da ita tace: ( Nakasance akwai azumin ramazhana akaina da'ake bina, bansamu damar ramawa ba sai awatan sha'aban, saboda matsayin Annabi Sallallahu Alaihi wasallam awajena).
Alhafiz ibnu hajar yace: Zamu fahimci kwadayin ramawarta acikin sha'aban, bai halatta jinkirta biyan bashin azumi ba, har zuwa wani ramazhan din ba.
Idan kuma mutum yajinkirta bashin azumi har wani ramazhan din bazai fita daka halaye biyu ba.
Nafarko: Yazama jinkirin akwai uzuri acikinsa, kamar mara lafiyan da cuta taci gaba ajikinsa har wani azumin yazo, wannan babu zunubi akansa wajan jinkirta azumin, domin shi mai uzurine, babu Abunda zaiyi saidai yarama azumin kawai.
Na Biyu: Yakasance jinkirin narashin uzurine, kamar wanda yasamu damar ramawa Amma yaqi ramawa harwani azumin yazo.
Wannan yanada zunubin jinkirinsa, malamai sunyi ittifaqi akan ramuwar tana nan akansa, saidai sunyi sabani akan *Shin wajibine yaciyar dakowanne miskini kowacce rana ko bazai ciyarba ramuwa kawai zaiyi?*
*Imamu Malik da shafi'i da Ahmad* suntafi akan zaiciyar, sunkafa hujjah dacewa hakika anruwaito daka wasu sahabbai kamar *Abu huraira da Ibnu Abbas* Allah yakara yarda dasu.
*Abu hanifa* yatafi akan ba wajibi bane ciyarwa akansa rama azumin kawai zaiyi.
Yakafa hujjah da cewa Allah bai Umarni ga wanda yasha azumi dakomai ba, sai rama azumin kawai, bai Ambaci ciyarwa ba.
Allah madaukakin Sarki yace:
ﻭﻣﻦ ﻛﺎﻥ ﻣﺮﻳﻀﺎ ﺃﻭ ﻋﻠﻰ ﺳﻔﺮ ﻓﻌﺪﺓ ﻣﻦ ﺃﻳﺎﻡ ﺃﺧﺮ ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ / 185 .
Wanda yake ahalin rashin lafiya ko ahalin tafiya saiya sha azumi, yarama awasu kwanakin daban.
*Duba Almajmu'u Na nawawi (6/366) da Al-mugny (4/400).*
Wannan zancen nabiyu shine imamul bukhari yazaba, acikin sahihin littafinsa yace:
Ibrahimun naka'iy yace:
Idan mutum ana binsa ramuwar azumi bai ramaba har wani ramazhan din yazo, zai azumin ne kawai bazai ciyar ba, ana Ambatan wata magana daka Abu huraira da ibnu Abbas cewa: Mutum zaiciyar tareda rama azumin, sai Bukhari yace; Allah bai Ambaci ciyarwa ba, kawai cewa yayi ( saiya rama awasu kwanaki daban).
SHaik Usaimeen ma yatabbatar da wannan maganar tarashin ciyarwa akan wanda yai sakaci bai rama bashin azuminda ake binsaba harwani azumin yazo.
*Duba littafinsa sharhin Mumti'i Ala zhadul mustaqni'i (6/451).*
Saboda haka rama azumin shine dole, amma idan mutum yahada ciyarwa kowacce rana darama azumin wannan abune mai kyau..
Saboda haka azumin yana nan akan wanda yai sakacin rama azumi har wani ramazhaan din yazo.
In aka gama azumin ramazhan bayan sallah sai yayi kokarin ramawa
Wallahu A'alamu.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ ﻧﺸﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ ﻧﺴﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﻧﺘﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ .

‎GA MA SU SHA'AWAR SHIGA WANNAN GROUP SAI A TURO DA CIKAKKEN SUNA ZUWA GA LAMBAR MU TA WHATSAPP
08087788208
08054836621
 *_GROUP ADMIN: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)