HUKUNCIN WANDA YA MUTU DA RAMUWAR AZUMI AKANSA


*HUKUNCIN WANDA YA MUTU DA RAMUWAR AZUMI A KANSA.*

https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBqfaiPwf28l

*TAMBAYA*❓

Assalamu Alaikum ya kokari allah ya taimaka yayana ne ya rasu sanadiyyar rashin lfy to ana binshi azumin shekara biyu bai samu halin rama azumin ba har allah ya dauki rayuwarsa to za,a rama mishi azumin ko baza,a rama ba sabida wasu suna cewa acikin ciwon ya rasu to amma kuma yana samun sauki sai kuma ya kwanta ciwon yana yawan taso masa baisamu lfy isasshiya ba balle ya rama har ya rasu ya matsayin ramuwar shi zamu rama mishine mu yan uwanshi ?allah ya taimaka


*AMSA*👇

Wanda yasha azumin Ramadana ko yasha wata rana daga cikin ranakun da yayiwa Allah bakance saboda wani uzuri daga cikin uzurai dake sanya mutum yasha azumin, sai kuma ya rasu, wato ajali ya cimmasa kafin gushewar wannan uzuri, ramuwa ta saraya a kansa, ba zaiyi wasiyya da cewar ayi masa ramuwa ba, ko a fitar masa da fidiya, to wannan zata kasance sadaka a gareshi. Saboda ibada sai da ikon yi, mara lafiya ko mai uzurin da shari'a tayiwa hanzari babu komai akansa.
.
Wanda yasha azumi saboda wani uzuri, sai wannan uzuri ya gushe da 'yan kwanaki wanda wadannan kwanaki sa iya isarsa da ya rama azuminsa, bai rama ba har mutuwa ta cimmasa, to wannan akwai ramuwa akansa, ramuwa bata saraya daga kansa ba, saboda ya rayu bayan gushewar uzurin tsawon kwanakin da yaci ace ya rama azuminsa.
Domin kuwa Allah Ta'ala yana cewa: "Wanda ya kasance daga cikinku bashi da lafiya ko yana halin tafiya ya rama azuminsa a bisa kididdigar kwanakin gaba (bayan gushewar uzurinsa kenan a bayan Ramadana)".
[Suratul Bakara, aya ta 185].
.
Misali, idan yasha kwanaki uku ko biyar, sai kuma ya rayu kwanaki takwas ko bakwai cikin koshin lafiya da ikon yin azumi bayan Idil Fitri (ranar karamar sallah), sannan sai ya mutu, to wannan ramuwa tana kansa, saboda ya rayu wasu kwanaki da Allah yake masa umarni da ya rama bashin azuminsa a cikinsu.
.
Anan anso ga musulmi ya gaggauta rama azumi na farilla don kada ajali ya cimmasa, ya kasance daga cikin masu sakaci, idan bashi da mai yi masa ramuwa sai abin ya zame masa hasara.
.
Wanda yasha azumi ya kasance yana da halin ramuwa, bai rama ba mutuwa ta riskeshi a wannan halin, magadansa ko wanda yake wakilinsa akan dukiyarsa zasu dinga ciyar da miskini a kowanne wuni, saboda hadisin Ibn Umar (R.A) cewa: Annabi (S.A.W) yace: "Wanda ya mutu ana binsa bashin azumi na wata, magadansa su ciyar da miskini a kowacce rana tsahon watan (ko iya kwanakin da yasha bai yi ba)".
Tirmizi da Ibn Majah ne suka fitar da wannan hadisi.
.
Saboda wannan hadisi ne jamhurum malaman mazhaba (mafiya rinjaye) suka dogara bisa cewa ba'a yiwa mamaci azumi, sai dai a ciyar a maimakonsa, koda yayi wasiyya da ayi masa azumin bai halasta ba.
Suna kara kafa hujja da hadisin Ibn Abbas (R.A) yace: "wani ba zai yiwa wani sallah ba, hakama wani ba zai yiwa wani azumi ba, sai dai wani ya iya ciyarwa a maimakon waninsa, kowacce rana mudu guda".
.
An rawaito daga Nana A'isha (R.A) tace: "kada kuyi azumi ga mamatanku, ku ciyar a maimakonsu".
Amma wasu da yawa daga mabiya mazhabar Imamu Shafi'i sun tafi akan halascin yin azumi ga mamaci, inda suka kafa hujja da hadisin Bukhari da Muslim daga Nana A'isha (R.A) tace, Annabi (S.A.W) yace: "Wanda ya rasu ana binsa bashin azumi, waliyyinsa ya rama masa".
A wata ruwayar kuma daga Bazzaru: "Idan waliyyinsa yana so ya iya masa ramuwar azuminsa".
.
An rawaito daga Bukhari da Imamu Muslim da lafazin Ibn Abbas (R.A) yace: "Wata mace tazo wajen Manzon Allah (S.A.W) tace, ya Rasulullahi, mahaifiyata ta rasu akwai azumin da tayi bakacensa akanta, na iya yi mata shi?
Sai Manzon Allah (S.A.W) yace: "Yanzu idan bashi ne akan mahaifiyarki zaki biya mata? Sai matar tace: "Na'am" sai yace: "don haka kiyi mata azumin da tayi bakacensa" (domin kuwa bashin Allah ne yafi cancanta a biya).
.
Allah yasa mu dace, ya kar6i ibadunmu.

Abba Ahmad Gwammaja

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)