*HUKUNCIN WA'AZIN MACE GA MAZA*
https://chat.whatsapp.com/IZhc4HXjGXFDOuOmx3ceZA
*TAMBAYA*❓
Assalamualaikum warahmatullahi
Malam inada tambaya?
shin yakamata mace tafita gaban maxa tana wa'axantarwa?
*AMSA*👇
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.
Asali abin da ya fi dacewa kuma aka fi so, shine namiji ya koyar da maza, mace ta koyar da mata, ta wa'azantar da su, saboda kulle kafar ɓarna, da zata iya saka sashe su ya fitinu da sashe, wanda hakan sai ya haifar da lalata ko makamancin haka. Idan ba haka ba, mace na iya wa'azi ga namiji kamar yadda namiji na iya wa'azi, wannan shine asali. Allah yace
(وَلۡتَكُن مِّنكُمۡ أُمَّةࣱ یَدۡعُونَ إِلَى ٱلۡخَیۡرِ وَیَأۡمُرُونَ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَیَنۡهَوۡنَ عَنِ ٱلۡمُنكَرِۚ وَأُو۟لَـٰۤىِٕكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ)
[Surah Aal-E-Imran 104]
Ayar bata iyakance jinsin da mai wa'azi zai kira ko yayi ma nasiha ba, kamar yadda bata ambaci maza ba kaɗai a fagen masu da'awa ba.
Amma idan hakan bai samu ba, toh babu laifi mace ta yi wa'azi ga maza ko namiji yayi wa'azi ga mata, kamar yadda muka gabatar, sai dai da sharaɗin idan hakan ba zai haifar da fitina ba, kuma babu wani zaɓi sai hakan.
Don haka eh, ya kamata mace tayi wa'azi ga maza, idan zata nisanta daga gare su, zata nisanci yin amfani da murya mai janyo hankali ko haifar da sha'awar ta. Allah yace
(.. فَلَا تَخۡضَعۡنَ بِٱلۡقَوۡلِ فَیَطۡمَعَ ٱلَّذِی فِی قَلۡبِهِۦ مَرَضࣱ وَقُلۡنَ قَوۡلࣰا مَّعۡرُوفࣰا)
[Surah Al-Ahzab 32]
Bayan haka sai idan zata ɓoye adon ta daga ganin masu sauraro, ma'ana ta lullube jiki da kwalliya ta, kuma zata sauke ganin ta kamar yadda Allah yace
(وَقُل لِّلۡمُؤۡمِنَـٰتِ یَغۡضُضۡنَ مِنۡ أَبۡصَـٰرِهِنَّ وَیَحۡفَظۡنَ فُرُوجَهُنَّ وَلَا یُبۡدِینَ زِینَتَهُنَّ إِلَّا مَا ظَهَرَ مِنۡهَاۖ....)
[Surah An-Nur 31]
Don haka dai idan har za'a amintu daga dukkan sabubban fitina da ɓarna ga al'umma, kuma sai idan babu wani Mallami namiji da yake masani a fannin da zata yi wa'azin, toh shike nan, ya halatta mace ta wa'azantar da maza kamar yadda muka gabatar, idan zata kiyaye ababen da shari'a ta wajabta a kan ta kuma ta kiyaye mutuncin ta.
Wallahu ta'aala a'lam.
*_Amsawa_* :
*Malam Aliyu Abubakar Masanawa*
Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
*_Group Admin: 👇_*
*MAL. HAMISU IBN YUSUF*