*MAKARANTAR AZUMI 002//*
📌 ```HUKUNCIN AZUMIN WATAN RAMADANA
```
1- Azumin Watan Ramadana rukuni ne daga cikin rukunnan Musulunci, Musulmi gaba-dayansu suna matsayi daya ne wajen sanin hakan; domin yana daga cikin abubuwan da suke dole a san su a Addini.
2- Kuma yana zama wajibi ne ga kowani Musulmi, mai hankali, wanda ya Balaga, mai lafiya, mazaunin Gida; Da ne ko Bawa, Namiji ne ko Mace, amma banda wacce take fama da Jinin Haila ko kuma Jinin Haihuwa.
Da za’a samu wani yayi musun wajabcin Azumin Ramadana, to wannan mutumi ya zama Arne, ya fita daga addinin Musulunci.
3- Yana daga cikin dalilan da suke bayani akan wajabcin Azumi, fadar Allah – madaukaki: ( _Ya waɗanda sukayi Imani! An wajabta muku Azumi kamar yadda aka wajabta akan waɗanda suke kafin ku, don ku zamto masu tsoron_ _Allah_ ) [Suratul Baqarah: 183].
4- A cikin Sunnah kuma Manzon Allah ﷺ Yace: “ _An gina Musulunci ne akan rukunnai guda biyar, Shaidawa babu abin bautawa da cancanta sai Allah, kuma Annabi Muhammad Manzon Allah ne, da tsayar da Sallah, da bayar da Zakka, da yin AZUMIN WATAN RAMADANA, da ziyartar Ɗakin Allah”._
[Bukhaariy da Muslim ne suka riwaito shi, daga Sahabi Abdullahi ɗan Umar]
*Twitter* 👇🏿
https://twitter.com/AnnasihaTv?s=09
*Telegram* 👇🏾
https://t.me/AnnasihaTvChannel