HUKUNCIN YIN ABOTA DA MASHAYIN GIYA KO KAYAN MAYE


HUKUNCIN YIN ABOTA DA MASHAYIN GIYA KO KAYAN MAYE

https://chat.whatsapp.com/Cnf26Q8MPqz9yUYU1nxqRq

 *TAMBAYA* ❓

Salamun alaikum dafatan Mallam yana cikin koshen lafiya Allah yasa haka amin. mallam inada tanbaya. Ina da wani aboki yana yawan shan giya kuma yana yin sallah akan lokaci nayi masa magana nace ya daina shan giya yaki dainawa.
To mallam ya kaga sallan wannan bawan Allah yake?.
Nagode sai naga amsanka


 *AMSA* 👇

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Maimakon yin tambaya game da sallarsa, abinda ya kamata kayi tambaya akansa shine 
 *"SHIN YAYA HUKUNCIN ABOTARKU A MUSULUNCI?".* 

Hakika bai halatta ga Mutum mumini ya rika yin abokantaka da Mashayi ba. Ina nufin mashayin giya ko Kwaya ko Weewi ko kuma duk wani abu mai bugarwa.

Manzon Allah (saww) yace "KADA KAYI ABOTA DA KOWA SAI MUMINI, KUMA KADA WANI YACI ABINCINKA SAI MAI TSORON ALLAH".
(Abu Dawud da Tirmidhiy ne suka ruwaitoshi).
Sannan Manzon Allah (saww) yace : "MUTUM YANA BISA ADDININ ABOKINSA NE. DON HAKA MUTUM YA DUBI WANDA ZAI YI ABOTA DASHI".
(Tirmidhiy da Abu Dawud ne suka ruwaitoshi).
Ga kuma hadisin da Annabi (saww) yake cewa "MUTUM YANA TARE DA WANDA YAKE SO".
Don haka bai halatta ka rika yin abota da mutumin dake shan giya ba. Giya tsinanniyar aba ce. Allah ya tsine ma giya kuma ya tsine ma masu shanta da masu sayar da ita, da masu dakonta, da masu tatsarta..
Game da Sallarsa kuwa, Komai yawan Sallarsa ba zata hana arubuta masa wannan alhakin shan giyar da yakeyi ba.
Kayi masa nasiha yaji tsoron Allah ya dena shan giya. Idan kuma bai ji nasiha ba, to ka gujeshi ka dena abotaka dashi. Saboda hujjar wadancan hadisai da na lissafa a sama, bai halatta gareka ka rika yin abota da Fajiri ba.
WALLAHU A'ALAM.

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Post a Comment (0)