SHIN HADISIN SALLAR JUMA'A KARFE :9:00 YA INGANTA ?
https://chat.whatsapp.com/Cnf26Q8MPqz9yUYU1nxqRq
*TAMBAYA* ❓
Assalamu alaikum, Da farko Allah ya saka ma malaman zauren nan da alkhairi, tambayata a nan ita ce, ya matsayin yin sallar juma'a da karfe 9:00 na safe kuma a wani hadisi aka samo yin haka kuma ingantacce ne ko kuma da''ifi ko maudu'i ne hadisin?.
Allah bada ikon amsawa dai dai (amin).
*AMSA* 👇
Wa alaikum assalam.
yin sallar juma'a kafin rana ta yi zawali ya zo a hadisi tabbatacce a sahihul Bukhari, saidai mafi yawan malamai ba ÅŸi aiki da shi,saboda ba akansa Annabi (s.a.w) ya dawwama ba,mafi yawan lokuta annabi yana yin sallar Juma'a ne bayan rana ta yi zawali.
Duba maslaha yayin aikata hukuncin sharia ginshiki mai zaman kansa a sharia, wannan yasa Annabi (s.a.w) ya ki sake ginin Ka'aba da mayar da ita yadda take a zamanin annabi Ibrahim don kar Kuraishawa su fitinu,Tare da cewa ya so hakan, amma sai ya bar shi saboda maslaha.
Wanda ya yi sallar juma'a kafin rana ta yi zawali sallarsa ta yi, saidai lura da yanayin mutane yana halatta barin abin da yake ba dole ba, kamar yadda aka rawaito sayyadina Usmanu ya daina Kasaru a hajji saboda wani bakauye ya zamar da sallolinsa na tsawon shekara kasaru duka, bayan ya koma gida, saboda aikin sayyadi Usmanu da ya gani.
ALLAH NE MAFI SANI.
Dr Jamilu zarewa.
Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕