YADDA AKE WARWARE SIHIRI

YADDA AKE WARWARE SIHIRI

https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURQQ

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum. Malam Dan Allah a ba mu shawara na kariya daga aljanu, ko sihiri da sauransu , kuma Wanda aka yi wa sihiri na rashin aure me yakamata ya yi? Ko na yawon banza?

*AMSA*👇

Wa'alaikumus Salam. Ina roqon Allah ya warware ma kowa matsalarsa, ƴar uwa yana daga cikin hanyoyin kariya daga sihiri kafin afkuwarsa:
1. Jin tsoron Allah da aikata dukkan wajiban da Shari'a ta wajabta.
2. Nisantar dukkan abubuwan da Allah ya haramta, da kuma tuba daga munanan ayyukan da mutum ya aikata.
3. Yawaita yin karatun Alqur'ani mai girma a kullum, ta yadda zai zama mutum kusan koyaushe zai zama cikin tsarki.
4. Kyautata yin addu'o'i na neman tsari, da yin sauran azkár waɗanda shari'a ta aminta da yin su, kamar su:
ﺑِﺴْﻢِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺍﻟﺬِّﻱ ﻻَ ﻳَﻀُﺮُّ ﻣَﻊَ ﺍﺳْﻤِﻪِ ﺷَﻲْﺀٌ ﻓِﻲ ﺍﻷَﺭْﺽِ ﻭَﻻَ ﻓِﻲ ﺍﻟﺴَﻤَﺎﺀِ ﻭَﻫُﻮَ ﺍﻟﺴَّﻤٍﻴﻊُ ﺍﻟﻌَﻠِﻴﻢُ .
A riqa karantawa sau uku a duk safiya da yammaci. Duba Abu Dawud 5088.
Da Karanta ayatul Kursiyyi a bayan idar da kowace sallah, da karanta ta a safiya da yammaci, da kuma lokacin barci.
Da karanta Qulhuwallahu Ahad, da Qul'a'uzu Birabbil Falaq, da Qul'a'uzubirabbin Nás. Sau uku a duk safiya da yammaci da lokacin barci. Da yin duk sauran zikirori da suka tabbata a Alqur'ani da Sunnah, kamar addu'ar shiga gida da na fita gida, da na shiga bayi da na fita, da na kwanciya barci da na tashi daga barci, da sauransu.
5. Karyawa da dabino guda bakwai kafin a ci komai a kowace safiya idan an sami dama, kamar yadda Annabi s.a.w. ya tabbatar cewa duk wanda ya yi hakan wata cuta ta dafi ko sihiri ba za ta same shi ba. Amma ita ruwayar Muslim ta ce dabinon Madina ne, kawai dai idan ba a sami ta Madinan ba a yi amfani da wadda ake da ita. Duba Bukhariy 5445. Muslim 2047.
In Allah ya so idan mutum ya lizimci waɗannan abubuwa cutarwar mai cutarwa ba za ta taɓa samun sa ba, sai dai abin da Allah ya qaddara masa na jarabawa, Allah ya kare mu.
*YADDA AKE WARWARE SIHIRI*
Yana da kyau a sani cewa; ba a warware sihiri ta hanyar sihiri, yin hakan haramun ne. Amma akwai hanyoyi guda huɗu ingantattu da Musulunci ya tanadar na warware sihiri amma za mu taqaita ne ga nau'i biyu kamar haka:
1. Ciro sihirin da ɓata shi idan an gano inda yake ta hanyar da shari'a ta halasta, wannan na daga cikin babbar hanyar yi wa wanda aka yi ma sihiri magani.
2. Yin Ruqya da shari'a ta yarda da shi, wannan shi ma yana da sigogi uku, amma za a taqaita a siga ɗaya, saboda kada rubutun ya yi yawa, ga shi kamar haka:
A sami busassun ganyen magarya kore guda bakwai, idan babu a sami ɗanyu, sai a daka shi ya zama gari, daga nan sai a sami ruwa tsaftatacce kimanin wanda zai isa wanka, sai a zuba a cikin magaryar da aka daka ɗin, daga nan sai a yi isti'aza a karanta waɗannan ayoyi a ciki:
1. Ayatul Kursiyyi, (ita ce aya ta 255 a suratul Baqara).
2. Sai a karanta aya ta 117 zuwa ta 122 na suratul A'araf.
3. Sai a karanta aya ta 79 zuwa ta 82 na suratu Yunus.
4. Sai a karanta aya ta 65 zuwa ta 70 na suratu Ɗaha.
5. Sai a karanta "Qul Yá'ayyuhal Káfirun", (suratul Káfirun).
6. Sannan a karanta "Qulhuwallahu Ahad".
7. Sannan a karanta "Qul'a'uzu Birabbil Falaq".
8. Sannan kuma sai a karanta "Qul'a'uzu Birabbin Nás".
Bayan an gama karanta dukkan waɗannan da aka lissafo, sai a tofa a cikin ruwan magaryan nan, wanda aka yi masa sihirin sai ya sha sau uku, daga nan sai ya yi wanka da sauran da ya rage. In Alah ya so idan aka yi haka sihirin nan zai lalace, idan kuma ana buqata za a iya maimaitawa har sau biyu ko fiye da biyun har zuwa lokacin da Allah ya sa cutar ta gushe. Haqiqa an jarraba da yawa kuma Allah ya sa an dace da shi. Allah ya qara tsare mu daga mugun ji da mugun gani.
Duba littafin Addu'a'u Minal Kitábi Wassunnah, Wal'Iláju Birruqa Minal Kitábi Wassunnah, shafi na 85 zuwa 103.
Allah ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.* ✍🏻

Don Allah Yan'uwa Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING, wasu da yawa zasu amfana.

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*

Post a Comment (0)