HUKUNCIN YIN SALLOLIN AZAHAR DA LA'ASAR BAYAN TSARKIN JININ HAILA A BAYAN LA'ASAR



HUKUNCIN YIN SALLOLIN AZAHAR DA LA'ASAR BAYAN TSARKIN JININ HAILA A BAYAN LA'ASAR

https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8qu9GT

 *TAMBAYA* ❓

Assalamu alaikum Mlm macece take haila sai tasamu tsarki bayan la'asar shin xayi sallar axuhur da la'asar biyu ne koya don Allah a taimakmn d amsa ngd


 *AMSA* 👇

Wa'alaikumussalam Warahmatullahi Wabarakatuhu

Malamai Sunyi maganganu guda uku (3) karkashin amsar wannan tambayan:

(1) Yana wajaba a kanta tayi sallar Azahar da La'asar , Wannan shine abinda aka ruwaito daga wasu daga cikin Sahabban Manzon Allah (S.A.W) da Tabi'ai kamar su Abdurrahaman bin Auf da Abdullahi bin Abbas da Abu Huraira Yaddar Allah ta kara tabbata a garesu, shine kuma Ra'ayin Mujahid da Dawus da Shaafi'i da Imamu Ahmad bin Hanbal da Lais bin Sa'ad da riwaya daga Malik bin Anas.Allah yajikansu da rahama.

(2) Yana wajaba a kanta tayi sallar La'sar ne kawai.Wannan shine abinda aka ruwaito daga Al-Hasanul Basri da Qatada da Abu Hanifa,Allah Ya yi musu rahama.Daga cikin dalilansu hadisin Manzon Allah ,(S.A.W):
ﻣﻦ ﺃﺩﺭﻙ ﻣﻦ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﺭﻛﻌﺔ ﻓﻘﺪ ﺃﺩﺭﻙ ﺍﻟﺼﻼﺓ، ‏( ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻭﺳﻨﻦ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ﻭﺳﻨﻦ ﺍﻟﻨﺴﺎﺋﻲ ).
Manzon Allah (S.A.W) ya yi bayani karkashin wannan hadisin wanda yasamu Raka'a daya a sallar da yayi cikin lokacinta to ya samu wannan sallar. Amma sallar da ta gabata bai riske lokacin ta ba saboda haka bata wajaba akansa sannan taya za ayi mu wajabta mishi yin ta.

(3) Idan lokacin da tayi tsarkin kafin sallar Magrib lokacin zai isa tayi sallar guda biyu ko Raka'oi guda biyar to yana wajaba tayi Sallar Azahar da La'asar Idan kuma zai isheta yin salla guda dayane kawai to zatayi sallar La'sar ne kawai,wannan shine maganar Malik bin Anas Da Auza'i, Allah yajikansu da Rahama.
Abinda wasu malamai suka rinjayar cikin maganganu ukun wanda muna tare dasu shine nafarko saboda shi yafi gamewa, Sai dai idan lokaci yakure mata to zata iya daukan maganan karshe da malamai suka yi.
ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ ﺃﻋﻠﻢ .
DR. NASIR YAHYA ABUBAKAR BIRNIN GWARI

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Post a Comment (0)