HUKUNCIN YIN SAMARI GUDA UKU GA BUDURWA



HUKUNCIN YIN SAMARI GUDA UKU GA BUDURWA 

https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8qu9GT

*TAMBAYA*❓

Salam, dan Allah malam ina neman karin bayani akan maganar danakeji a bakin mafi yawan iyaye suna cewa yarinya budurwa sai ta samu manema 3 kafin ta zabi guda 1.
Abisa fahimta ta malam ina ganin bai dace mace ta tsaya jira ba har wai sai tasami samari 3 da zarar ta samu 1 wanda aka yadda da addininsa da halayensa kamar yadda musulunci ya tanadar sai a tsayar da magana akansa.
Amma a wannan lokaci zakaga yarinya budurwa suna tare da saurayi kimanin shekara 1 sannan hakan bai hanata kula wasu ba shi zaisa a ransa ya samu matar aure sun gama fahimtar juna amma da zarar wani yafito sai kaga iyaye suna cewa ai dama mace addinin yabata damar sauraren manema 3 kafin ta tsayar da guda 1 a ciki basa duba waccan dadewar dana bayan yayi yana nema.
Awasu lokutan ma har manya sun san da maganan daga both side koda dai ace ba'a kawo kudin aure ba ko sa rana amma ni ina ganin still haka din bai dace ba.
Dan Allah malam yaya abin yakene ???
Nagode ka huta lfy.


*AMSA*👇

Eh babu laifi domin mace samari da yawa sunce suna sonta.
Amma shari'a bata bayar da dama akan ta tsaya dasu gaba dayan suba.
Ita macen zata iya sanya wani dan uwanta yayi mata bincike akan wanda hankalinta yafi kwanciya dashi a cikinsu.
Addini yabayar da za6i akan cewa:
Zaka iya auren Mutun mace ko namiji domin abubuwa kamar haka:
1. Addini.
2. Kyau.
3. Nasaba.
4. Dukiya.
5. Tarbiya.
Amma daga Qarshe sai akace yafi kyau ku aura domin addini da tarbiyar, saboda sune kan gaba.
Bai kamataba ga iyaye su amsa maganar wani mutum a shafe samada shekara guda yana soyayya da 'yarsu daga baya suce zasu rabasu batareda wani dalili mai Qarfiba, Hakan cutarwane.
Idan basu yarda dashi ba meyasa suka amshi batunsa tun farko ?
Sannan idan akace baza'a auri kowaba sai mai addini to sukuma sauran mutane yaya za'ayi dasu ???
Yakamata mudinga yin aiki da lura.
Allah ka aurar ga matasanmu ga ma'aurata nagari.
WALLAHU A'ALAM.

Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING, wasu da yawa zasu amfana.

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)