ZAN IYA YIN ADDU'A ALLAH YA DAUKE RAINA
https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8qu9GT
*TAMBAYA*❓
1. Assalamu alaikum Mallam tambaya ne shine Allah mutum za'iya adua Allah ya dauki ransa.Allah yaqara wa mallam ilimi.
*AMSA*👇
Akwai Hadisi Ingantacce Manzon Allah saw Yace, KA DA DAYANKU YAYI BURIN MUTUWA SABIDA WATA CUTA DA TA SAME SHI, IDAN HAR BA MAKAWA SAI YAYI ADDA'A, TO YA CE YA ALLAH IDAN MUTUWA CE TA FI ALKAIRI A GARE NI, ALLAH KA KARBI RAYUWA TA. IDAN KUMA RAYUWA TA CE TAFI ALKAIRI A GARE NI, YA ALLAH KA RAYA NI.
Ka ga kenan ba Maganar ka yi Wa kanka Irin wannan Mummunar Addu'ar. Sabida Allah ne ya san Abinda zai faru a Nan gaba.
Ba Mamaki zai yaye maka Wannan Abinda ya same ka, ko kuma ya Maida ma da Abinda ya fi shi Alkairi. Ko kuma Sakamakon wannan Kuncin zuciyar ya saka ma da gidan Aljannah. Amma sai idan ka yi Hakuri.
Hadisi ya Tabbata. Wata mata ta zo wajen manzon Allah saw ta ce Ya manzon Allah saw!!! Ka Roka Mun Allah ina da cutar farfadiya, ina yawan Faduwa Akan ya yaye min. Sai manzon Allah saw ya ce da ita. IDAN KIN SO ZAN ROKA MIKI ALLAH ZAI YAYE MIKI. IDAN KUMA KIN SO A BARKI DA JINYAR KI, IDAN KIKA MUTU ZAKI SHIGA ALJANNAH. Sai wannan Matar ta ce a Barni da Jinya ta idan na Mutu in Shiga Aljannah.
Sai Tace Amma ya Manzon Allah ka Roka Mun Allah idan na fadi zanen da yake jiki Na ya dena Kwancewa daga jikina. Sakamakon Murginawa da Nake yi, idan na tashi sai in Ganni Tsirara. Sai Manzon Allah saw ya Roka Mata Allah. Tin daga Wannan Lokacin idan ta Fadi, zanen Jikinta Ba ya Fita.
Ka ga kenan Ya Kamata Muke Hakuri Muna Maidawa Allah Lamuranmu Gabaki daya Idan wani Abu ya same Mu wanda ya sanya Mu a Cikin Tsanani ko Damuwa.
Allah shine Masani.
Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕