INA DA SAURIN FUSHI IDAN AKA ƁATA MIN RAI SA'ANNAN DA SAURIN KUKA, MEKE JAWO HAKAN?
https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV
*TAMBAYA*❓
Assalamu akaikum Malam, ina neman shawara a kan wani hali da nake da shi tun ina karama har zuwa girma na ban daina ba sai dai ya ɗan ragu, wannan hali shine saurin fushi da kuka in aka bata min rai sai inyi fushi ko, kuka, ko naga wani cikin mawocin hali, ko naga wani yana kuka, ko naji wani labari mai ban tausayi, da sauran su in ban yi fushi to zan yi kuka, menene haka raunin zuciya ne dan Allah malam ka bani shawara yadda zan yi nagode.
*AMSA*👇
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah.
Fushi dai abu ne da aka halicci Ɗan Adam da shi, siffa ce daga cikin siffofin bashariyya, sai dai iri biyu ne, akwai wanda shari'a tayi rangwame a kan shi kuma abun yabo ne ma. Misali, mutum ya yayi fushi saboda an ci mutuncin Annabi ko addinin musulunci ko shari'ar Allah ko kuma an taɓa girman Allah, fusata saboda ɗaya daga waɗannan ya zamo wajibi kuma abin so ne. Annabi sallallahu alaihi wa sallama yana fushi ne kawai idan aka taɓa addinin Allah, ba in aka taɓa mutuncin shi ba. Allah ma yana fushi da mutanen banza, irin fushin da ya dace da Jalalar Shi Azza wa Jalla.
Amma fushi irin naki, shine fushi na zargi a shari'a, kuma tayi hani daga barin shi, domin fushi irin naki daga shaiɗan ne. Maganin shi, a duk lokacin da aka faɗa maki abin da ya fusata ki, sai ki nemi tsarin Allah daga shaiɗan. Idan fushin ya tsananta, sai kiyi alwala kiyi sallah insha Allahu zaki rabu da shi, saboda shaiɗan yana tserewa daga bigiren da aka ambaci Allah.
Shawara a nan ita ce, ki nisanci haɗuwa ko zama da wanda zai ɓata maki rai, sai dole. Ki koyi haƙuri, saboda koyon shi ake yi, sai Allah ya mayar dake mai haƙuri, Annabi yace wanda ya koyi hakuri Allah zai haƙurtar da shi
عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ أَنَّ نَاسًا مِنَ الأَنْصَارِ سَأَلُوا رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَأَعْطَاهُمْ ثُمَّ سَأَلُوهُ فَأَعْطَاهُمْ حَتَّى إِذَا نَفِدَ مَا عِنْدَهُ قَالَ: ((مَا يَكُونُ عِنْدِي مِنْ خَيْرٍ فَلَنْ أَدَّخِرَهُ عَنْكُمْ وَمَنْ يَسْتَعْفِفْ يُعِفَّهُ اللَّهُ وَمَنْ يَسْتَغْنِ يُغْنِهِ اللَّهُ وَمَنْ يَتَصَبَّرْ يُصَبِّرْهُ اللَّهُ وَمَا أَعْطَى اللَّهُ أَحَدًا مِنْ عَطَاءٍ أَوْسَعَ مِنَ الصَّبْرِ)).
Abin da zai taimaka maki wajen koyon haƙuri shine kullum ki tuna cewa ke ma, kina saɓa ma Allah da Manzo, iyayen ki, Mallaman ki da waɗanda kike mu'amala da su, amma suna haƙuri da ke. Idan don an taɓa mutuncin ki ne, toh ki tuna an taɓa mutuncin wanda yafi ki mutunci.
Shi kuwa saurin kuka na nuna rauni, karayar zuciya ko tsananin fushi, kuma kuka saboda tsananin ɓacin rai na haifar da illa ga zuciya. Amma kuka saboda kin ga wani cikin mawiyacin hali ko yana kuka, na nuna tausayi ne da karayar zuciya. Irin wannan imani ke saka haka, Annabi ya kasance yana zubar da hawaye saboda ya ga wani cikin yanayi matsananci, saboda tausayi
عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: ((وُلِدَ لِيَ اللَّيْلَةَ غُلاَمٌ فَسَمَّيْتُهُ بِاسْمِ أَبِي إِبْرَاهِيمَ)). فَذَكَرَ الْحَدِيثَ قَالَ أَنَسٌ لَقَدْ رَأَيْتُهُ يَكِيدُ بِنَفْسِهِ بَيْنَ يَدَيْ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَدَمَعَتْ عَيْنَا رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ: ((تَدْمَعُ الْعَيْنُ وَيَحْزَنُ الْقَلْبُ وَلاَ نَقُولُ إِلاَّ مَا يَرْضَى رَبُّنَا إِنَّا بِكَ يَا إِبْرَاهِيمُ لَمَحْزُونُونَ)).
Ana son irin wannan kukan, ba abin zargi bane a musulunci, ko kuma kuka yayin da ake karanta alqur'ani ko aka ambaci Allah, shari'a tayi umarni muyi haka, kuma alama ce ta mutanen kirki
(أُو۟لَـٰۤىِٕكَ ٱلَّذِینَ أَنۡعَمَ ٱللَّهُ عَلَیۡهِم مِّنَ ٱلنَّبِیِّـۧنَ مِن ذُرِّیَّةِ ءَادَمَ وَمِمَّنۡ حَمَلۡنَا مَعَ نُوحࣲ وَمِن ذُرِّیَّةِ إِبۡرَ ٰهِیمَ وَإِسۡرَ ٰۤءِیلَ وَمِمَّنۡ هَدَیۡنَا وَٱجۡتَبَیۡنَاۤۚ إِذَا تُتۡلَىٰ عَلَیۡهِمۡ ءَایَـٰتُ ٱلرَّحۡمَـٰنِ خَرُّوا۟ سُجَّدࣰا وَبُكِیࣰّا ۩)
[Surah Maryam 58]
Abin da zai taimaka maki wajen raba ki da sauri fushi, shine yawaita Istighfari da karanta alqur'ani, salatin Annabi da koyi da mutane na gari magabata da na wannan zamani. Yawan tuna mutuwa da ƙididdige laifukan ki zai taimaka maki wajen raba ki da saurin fushi. Lazimtar azkar na safe da yamma, zama da alwala, da mutanen kirki, da majalisin ilmi, da ƙoƙarin bita da ɗabbaƙa abin da ki ka koya a makaranta, a aikace, zai taimaka maki wajen rage maki saurin fushi ko ya raba ki da shi.
Na daga abin da zai raba ki da saurin fushi, tuna natijar shi, ita ce nadama, shi yasa Annabi yayi umarni cewa kar kayi fushi.
Wallahu ta'aala a'lam.
*_Amsawa_* :
*Malam Aliyu Abubakar Masanawa*