RUBUTUN ‘HAUSA NOVELS’ DOMIN FAƊAKARWA
https://chat.whatsapp.com/BsuVPYdzZY7C1Sv0lgoNES
*TAMBAYA*❓
_Assalamu Alaikum._
Malam kamar yadda ka taɓa amsa tambaya game da _‘novels’_ shi ne muka samu tambaya makamanciyar wannan. Ga ta kamar haka:
Shin ya halatta rubuta labari ma’ana: Hausa novel wanda babu batsa, kuma ba don nishaɗi aka yi shi ba, sai tarin faɗakarwa a ciki?
Kamar misali wanda aka yi mai suna *Naƙasasshe Ma Mutum Ne* . Labari ne shi ma kuma an yi jan hankali ne kan al’umma ta yadda suke gudun auren naƙasassu, sannan marubuciyar ta yi amfani da aya da hadisai domin faɗakar da mutane.
Sai kuma wani da aka nuna illar rashin yin kyakkyawan bincike da iyaye ba su yi yanzu wajen aurar da ’ya’ansu.
Shin malam, irin waɗannan sun halatta, ko kuwa gaba-ɗayansu haram ne?
*AMSA*👇
_W Alkm Slm W Rhmt Laah_
Abin da nake cewa a kullum shi ne:
[1] Shin Alqur’ani da Hadisai Sahihai ba su isa su shiryar da al’umma ba ne, sai dole an ƙirƙiro irin waɗannan hanyoyin na tatsuniyoyi an jingina su da addini?
[2] A sakamakon sako-sako da wannan matsalar ce fa a yau muka samu wasu ƙungiyoyin na mawaƙa da makiɗa da ’yan drama iri-iri waɗanda suka karkace daga hanyar gaskiya, har abin ya kai ana samun mawaƙan da har Allaah Ta’aala suke yi wa waƙe-waƙe da kiɗe-kiɗe da sunan addini!
[3] Haka aka samu waɗanda suke da’awar cewa hanyar su ta amfani da drama ko fim domin faɗakar da jama’a ta fi hanyar da Malamai na-Allaah masu wa’azi su ke kai! Har ma suke ƙalubalantar Malaman da cewa: A shiga gidajen jama’a a duba mana: Kasusuwan wa’azi ko karantarwa ko faɗakarwarsu ne suka fi yawa ko kuwa kasusuwan Malamai masu wa’azi da koyarwar?!!
[4] Sannan kuma wai mutum nawa ne a gaskiya suka rabu da hanyoyin ɓata da ɓarna, suka dawo suka kama hanyar gaskiya saboda sun amfana da irin waɗannan hanyoyin na tatsuniyoyi da drama da makamantansu?!!!
[5] A taƙaice dai: Waɗannan hanyoyi a fahimtata ba hanyar gyara al’umma ba ce. Hanyoyin da Annabawa da Manzanni da Malaman Sunnah Magabata da na-yanzu suka bi wurin karatarwa da faɗakar da al’umma su ne kaɗai hanyoyin bi domin kaiwa ga nasara, _in sha’al Laah._
Amma dai kowa ya san cewa, bayan an gama duk wannan hayaniyar ta duniya, to fa akwai ranar da kowannenmu zai tsaya a gaban Ubangijin Halittu, kuma ya yi bayanin yadda ya gabatar da rayuwarsa. Zai sani a ranar nan idan hanyar da yake bi a yau ita ce hanyar da Allaah ya yi umurni da a bi ta, ko ba ita ba ce!!!
_Wal Laahu A’lam._
*Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy*
Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕