MIJINA YANA SON KISS AMMA BA YA TSAFTACE BAKINSA, HAKAN YA SA BA NA SO, MENENE HUKUNCINA?
*TAMBAYA* :❓
Assalamu Alaikum malam, 'yar uwata ce mijinta yake son kiss ita kuma ba ta yi masa saboda ba ya son tsaftace bakinsa shi ne yake jin haushinta, ita kuma abin yana damunta tana ganin kamar ta shiga hakkinsa shi ne take so ta ji menene hukuncinta kuma ya za ta yi ta samu mafita?
*AMSA*👇
Wa'alaikumus salam, abin da ya kamata shi ne ta faÉ—a masa gaskiya cewa ita ba kiss É—in ne ba ta so ba, ita da shi É—in su riqa tsaftace bakinsu kafin su kai ga sumbantan junansu, ina ganin kamar hakan shi ne mafita, saboda idan aka cigaba da yi masa kawaici ba zai gane dalilin da ya sa ba ta ba shi haÉ—in kai ba, kuma kullum zai ta jin haushinta, ita kuma ba za ta fita daga damuwar da take ciki ba. Amma idan ya qi gyarawa tana da uzuri har a wurin Allah, saboda tsafta yanki ne na imani kamar yadda hadisin Muslim ya tabbatar.
Allah S.W.T ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
https://t.me/joinchat/Bdi85VSaiLc5NGQ0