ZAN IYA YIWA YARO TSARKI BAYAN NAYI ALWALA



ZAN IYA YIWA YARO TSARKI BAYAN NAYI ALWALA
:
.
*_TAMBAYA_*❓
:  
_Assalamu alaikum Dan Allah tambayata anan itace mutum ya gama alwala zai iya yiwa yaro tsarkin kashi??_
:
_*AMSA:*_👇
:
_Alwala bata lalacewa a dalilin wanke wa yaro Kashi ko fitsari ko wata kazantar jikinsa. Saboda taba najasa baya bata alwala, amma wajibi ne mutum ya wanke hannunsa da kyau bayan ya yiwa yaro ko yarinya tsarki._

_An fada acikin *Fataawa Al-lajnatu al-da'imah* cewa:_
_Alwala bata lalacewa saboda wanke najasa daga jikin wanda yayi alwala ko waninsa._
_*(Majallat Al-buhuut al-islamiyyah, 22/62).*_

_Taba wasu medical equipments ko shiga cikin toilet da kafa ba takalmi baya lalata alwala. Haka kuma idan akwai najasa a floor din toilet din kuma mutum ya shiga ba takalmi a kafafunsa, to alwalarsa bata lalace ba, amma zai wanke kafafunsa._

_Taba kayan yaro da suka jiqe da fitsari ko wata kazanta, wannan baya bata alwala, amma mutum zai wanke duk sashen jikinsa da ya shafi kayan masu fitsari ko kazanta._
_*(Majmu'ul Fataawa bin Baaz, 10/141).*_

_An tambayi *Sheikh ibn Uthaimin (rahimahullah)* akan macen da ta wankewa yaronta kazanta (Kashi ko fitsari) a lokacin tanada alwala, shin zata sake alwala ne??_
Sai yace:
_Idan mace ta wankewa yaronta ko yarinyarta kazanta kuma ta taba al'aurarsa, bazata sake alwala ba, amma zata wanke hannunta._

_Saboda shi taba al'aura batareda jin sha'awa ba, baya lalata alwala. A bayyane yake cewa idan uwa tana wanke al'aurar 'yarta ko danta, tinanin sha'awa baya taba zuwa a zuciyarta. Saboda haka idan ta wankewa yaronta ko yarinyarta kazanta, to zata wanke hannunta ne saboda kazantar da ta shiga hannun, amma bazata sake alwala ba._
_*(Majmu'ul Fataawah ibn Uthaymeen, 11/203).*_
:
```Allah ta'ala yasa mudace```
:
:
_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​*_
zaku iya samu wannan group na telegram da na Facebook ta wannan hanyar👇

 *Telegram*👇
https://t.me/joinchat/Bdi85VSaiLc5NGQ0

 *Facebook*👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)