MU RIƘA NEMAWA 'YAN UWANMU GAFARA


#MU RIQA NEMAWA YAN UWANMU GAFARA

Yana cikin alamar sun albarka da kaunar masu imani ka riqa nema masu gafara awajan Allah shiyasa Allah da kansa yayi umarni ga masu imani akan su riqa nemawa kansu gafara kuma su riqa nemawa sauran masu imani gafara.

Allah yana cewa:
(فَاعْلَمْ أَنَّهُ لَا إِلَٰهَ إِلَّا اللَّهُ وَاسْتَغْفِرْ لِذَنبِكَ وَلِلْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ ۗ وَاللَّهُ يَعْلَمُ مُتَقَلَّبَكُمْ وَمَثْوَاكُمْ)

*(Sabõda hakaa ka sani, cẽwa bãbu abin bautãwa fãce Allah,kuma ka nẽmi gãfara ga zunubin,ka, (kuma sabõda mũminai maza da mũminai mãtã kuma Allah Ya san majũyaiku da mazauninku)*.
@محمد (19) Muhammad

Kuma Allah yayi yaba masu nemawa magabatansu masu imani gafara sai Allah yace:
(وَالَّذِينَ جَاءُوا مِن بَعْدِهِمْ يَقُولُونَ رَبَّنَا اغْفِرْ لَنَا وَلِإِخْوَانِنَا الَّذِينَ سَبَقُونَا بِالْإِيمَانِ وَلَا تَجْعَلْ فِي قُلُوبِنَا غِلًّا لِّلَّذِينَ آمَنُوا رَبَّنَا إِنَّكَ رَءُوفٌ رَّحِيمٌ )

*(Kuma waɗanda suka zõ daga bãyansu, sunã cẽwa,"Yã Ubangijinmu! Ka yi gãfara a gare mu, kuma ga 'yan'uwanmu, waɗanda da suka riga mu yin ĩmãni, kada Ka sanya wani ƙulli a cikin zukãtanmu ga waɗanda suka yi ĩmãni.Yã Ubangijinmu! Lalle Kai ne Mai tausayi,Mai jin ƙai)*
@الحشر (10) Al-Hashr

Annabi SAW ya kwadaitar damu akan yawan nemawa yan uwamu gafara dan samu falala mai yawa awajan Allah.

1-Manzon Allah SAW yana cewa;
*(Duk wanda ya nemawa masu imani maza da mata gafara Allah zai rubuta ladar aiki mai kyau ga kowane mai imani da ya nema masa gafara)*.
@حسنه الألباني في
 صحيح الجامع - قم: (6026)

Duk wanda ya nemawa mai imani gafara,shima Allah zai sanya Mala'ika ya nema masa gafara.

Manzon SAW yana cewa:
*(Babu wani bawa da zaiyiwa wani bawa addua a bayan idonsa wato bansan yayi masa wannan adduar ba,face wani Mala'ika yace masa kaima Allah ya baka irinsa)*.
@صحيح مسلم - رقم: (2732)

Allah kayi gafara da rahama da jinkai ga dukkan masu imanin duniya baki daya.

_ya Allah kayi rahama da yafiya da gafara ga dukkan masu imani da suka rigamu gidan gaskiya,ka sanya su a aljanna madaukakiya_

*_Allah kasa mu cika da imani idan tamu tazo_*
Post a Comment (0)