MUNA JINKIRTA WANKAN JANABA HAR ZUWA BAYAN ASUBA


*MUNA JINKIRTA WANKAN JANABA ZUWA BAYAN ASUBA,A WATAN RAMADANA ?*

*Tambaya:*

Assalmu alaikum, malam ina da tambaya shin meye hukuncin matan da za su sadu da mijinsu lokacin azumi, amma ba za su yi wanka ba har sai alfijir ya fito, shin yaya
matsayin azumin su yake.? Nagode

*Amsa:*

Wa alaikum assalam, ya halatta mace ta sadu da mijinta su jinkirta wanka zuwa bayan ketowar alfijir a watan Ramadhana, a zuminsu kuma ya inganta, saboda Annabi S.a.w yakan yi haka da matansa, kamar yadda iyalan sa A'isha da Ummu Salama suka rawaito hakan, kuma Muslim ya fitar da riwayar a Sahihinsa a hadisi mai lamba ta: 1874.

Allah ne mafi sani

21/05/2016.

*Amsawa:* Dr. Jamilu Zarewa.
Post a Comment (0)