NA CI ABINCI BAYAN ALFIJIR YA KETO

*NA CI ABINCI BAYAN ALFIJIR YA KETO !*

*Tambaya*

Assalamu Alaikum Malam jiya bayan na gama cin abinci, sai na samu ashe alfijir ya keto, tun kafin na fara ci, saidai Allah ya sani, na ci ne a rashin sani, ko ya zan yi yanzu ?

*Amsa*

Wa'alaikum Assalam, 
To malam mutukar ba da saninka ka yi haka ba, to
azuminka ya inganta, domin duk lokacin da mai azumi ya yi kokwanton huduwar alfijir, to ya halatta a gare shi ya ci abinci, saboda wanzuwar dare shi ne asali, kamar yadda Ibnu-abbas yake cewa : "Allah ya halatta mana cin abinci - a Ramadhana- mutukar mun yi kokwanton hudowar alfijir", sai dai in da zai yi kokwanton faduwar rana to bai halatta a gare shi ya Ci abinci ba, saboda wanzuwar ranar shi ne asali.

Allah ne mafi sani 

20/6/2015.

*Amsawa:* Dr. Jamilu Zarewa.

Post a Comment (0)