MUTUM YANA SIYAR DA ABIN DA YAKE MALLAKA NE?

MUTUM YANA SIYAR DA ABIN DA YAKE MALLAKA NE?

*Tambaya*

Assalam sheikh barka da warhaka tambayane akan
Ma aikatane tayi gwanjon kayayyakinta ga ma aikata sai mutum ya tallata wani na waje amma yayi kari akan farashin da akayanke wa kayan,menene hukuncinsa?

*Amsa*
Wa'alaykumussalam

Yana daga cikin sharadin cinikayya shine mutun ya saida abinda yake mallakar sa ne cikakkiyar mallaka, haka nan shari'a ta hana mutun ya saida abinda ba yada shi /bai zo hannun sa ba, manzon Allah ya hana irin wannan cinikin a cikin hadisin Hakeem bn Hizaam wanda yake cikin sunan na Abu dauda 3503, Tirmizi 1232 Nasa'i 4613 Ibn majaa 2187. Da hadisin Abdullahi bn Amr wanda shima yana cikin wadan nan masadir din... 

Ibn qayyin a cikin littafin sa Zadul-Ma'ad 5/808 yana bayani akan wadan nan hadisan biyu sai ya ce " manzon Allah ya hana mutun ya saida abin da baya dashi /ba mallakar sa ba, domin cikin ya kunshi wani nau'i na garari (rudu)... 

Don haka dai hakan bai halatta ba, amma idan an bashi wakilci ne bisa sharadin ya saida abin ya kawo kudi kaza duk abinda ya dora a sama nashi ne toh wannan ya halatta. 

Wallahu A'alam

*Malam Nuruddeen Muhammad (Mujaheed)*

07/01/2021

ZaKu iya Bibiyar Mu a 

Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248

Post a Comment (0)