MATA KU DAINA RUDUWA DA ‘YAN BOKO AQIDAH, WADANDA KE KOKARIN KASHE MUKU AURE !!!
.
Acikin kwanakin nan munci karo da vedeo na wata Mace Bagidajiya tana Kiran Mata da su hakikance wajen bude wayoyin mazajen su ko ta halin kaka, take Kira da cewar duk namijin da ya haramtawa Matarsa ganin cikin wayarsa ba abokin rayuwa bane.
.
Tace ita idan mijin ta bai bari ta duba wayar sa ba akwai matsala... Abu na farko a wannan gabar ta aika saƙon.
.
Ta bar kowacce mace da ta dauki shawarar ta cikin ruɗani na zabar kalar matsalar da zata faɗa a yunkurin binciken wayar mijin ta.
.
Abu na biyu ko namiji bayi da gaskiya ba inda aka ce sai kin duba wayar sa domin addini bai yarda da abunda zai kawo tashin hankali ba har ya kai ga mutuwar aure.
.
Karya take yi ta rasa aurenta tana Kiran ku Kuma ku kashe auren ku, ku zamto irinta.
.
Munga Mata da dama suna gaskata ta, toh wallahi kuyi karatun ta nutsu matukar kuka biye Mata zaku dawo zawarawa, yayanku su Zama Kara zube.
.
Waye yace wajibi ne sai Matar mutum tasan sirrin mijinta gaba daya ??? Me yasa addini yayi hani da zato acikin aure, me yasa addini ya ambaci kada ayi bincike a wasu wurare, saboda a zauna lafiya.
.
Haka kuma shi namiji yanada mu'amuloli da yawa, ba sirrin sa kawai ne a hannun sa ba, ashe kenan ba lallai ne komai na shi sai kin sani ba ta yanda zaki iya sanin sirrin wasu. Ko ma dai meye, da sanin da rashin sanin ba abund zai ƙare ki, ke dai kiyi kokari ki zauna lfy da mijin ki, domin rayuwar zawarci ba ita ce duk mai hankali ke so ba.
.
Toh ‘Yar-uwa Ina mai tabbatar miki idan kika sanyawa zuciyarki dole sai kin bincika wayar mijinki toh kina gab da zamowa Bazawara kamar wannan Mata da take hura Miki kunne take aika miki da sakon Shaidan, ita ma Karan kanta Shaidan ce, domin Shaidan Babban burinsa shine ya shiga tsakanin ma’aurata.
.
‘Yar-uwa ina Kira zuwa gare ki, ki sani cewa auren nan ibadah ne Kuma zaman hakuri Shima ibadah ne, ki tsarkake zuciyarki ki cire zato da zargi acikin rayuwar aurenki kiyi Zama da zuciya guda daya, idan kika yi haka ALLAH zai zame miki gata Kuma bazai bari Maigidanki ya cutar dake ba koda ya cutar dake a kasa toh na sama Kuma zai Miki sakayya.
.
Mu Ahlus-sunnah fatan mu da burin mu acigaba da Raya Sunnar Annabi ﷺ har illa Maashaa ALLAH, Kuma ba zamu zuba ido masu mummunar Aqidah su nemi wargaza wannan Sunnar ba, ALLAH bazai taba basu Nasara ba.
✍️ Faridah bintu Salis (bintus Sunnah)
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248