﷽
اَلسَلامُ عَلَيْكُم وَرَحْمَةُ اَللهِ وَبَرَكاتُهُ
Daga Zauren
*📌Albahral Ilmu🌴*
*_YA HALARTA NA SADU DA MATATA TANA DA JUNA BIYU?*
*TAMBAYA*❓
Assalamu alaikum
Malam idan mace tanada juna biyu tsawon wata 6 ya halasta Mijinta yayi kwanciyar sunnah da ita kuma wace illa ce jinjirin zai samu?
*AMSA*👇
ﻭﻋﻠﻴﻜﻢ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻭﺭﺣﻤﺔ ﺍﻟﻠﻪ .
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ ،
Ya halasta Miji ya sadu da matarsa mai dauke da juna biyu a duk lokacin da yake so, koda cikin ya wuce watanni 7, sai fa idan yin hakan yana cutar da matar, haramun ne Miji yayi kowane irin abu da zai cutar da Matar sa. Idan yin saduwar bazai cutar da matar ba, amma akwai wahala agareta, toh yafi dacewa Mijin ya hakura kar ya sadu da ita, domin kauracewa aikata duk abinda zai wahalar da ita, wani nau'i ne na zamantakewa da ita cikin aminci da kyautatawa. Allah (S.W.T) yana cewa
.....وعاشروهن بالمعروف....
(النساء /19)
_......Kuma kuyi zamantakewa da su da alkhairi......._
Sannan babu wata illa da saduwa da mace mai juna biyu yake haifarwa jinjirin dake a ciki.
Amma haramun ne Miji ya sadu da matarsa a lokacin da dayan su (Miji ko Mata) yake cikin ihraam na aikin hajji ko Umrah, ko kuma dayan su yana azumi da rana, amma zasu iya saduwa da dadaddare bayan sun buda baki.
Haka kuma haramun ne saduwa da mace idan tana cikin jinin Nifaas.
Haka kuma haramun ne Miji ya sadu da matarsa a lokacin da take cikin haila har sai ta samu tsarki tayi wanka.
Idan tana haila Mijinta zai iya jindadi da ita amma ba ta farjinta ko duburar ta ba. Saboda *Manzon Allah (Sallallahu alaihi wa sallam)* yace;
_لقول النبي صلى الله عليه وسلم: اصنعوا كل شيء إلا النكاح._
*رواه مسلم (الحيض /455)*
_Ku aikata komai, amma banda shiga (saduwa ta farjinta)._
_*(Muslim, Al-hayd, 455)*_
فتوى الشيخ ابن عثيمين . فتاوى العلماء في عشرة النساء ص/ 55.
_*(Fataawa Shaykh Ibn Uthaymeen, Fataawa Al-ulama' fii Ashratin Nisaa', shafi na 55).*_
والله أعلم،
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.
Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
*07064746551*