Gaskiyar Kenan

*GASKIYAR KENAN!* - _Mal Mustapha Ja'afar T/Jukun Zaria_
*_“Babu ruwana da siyasar PDP, babu ruwana da siyasar APC. Abunda ya dame ni shine addinin Annabi Muhammad(SAW)”-DR. AHMAD GUMI_*
Aato! Idan kaga waɗanda ake fatan su zama a gaba wajen damuwa da addinin Allah amma basu damu da shi ba, saima dasu da yayansu ne suke FITSARA da LALATA iri-iri a idon duniya, to kai musulmi ya kamata ka kama addinin Allah QAM-QAM ko ka gama lafiya.
An hana wata takardar shaidar gama karatun lauya saboda tasa HIJABI basu damu ba, a embasi na Nigeria dake Saudiyya kuma ance wata sai ta daga NIQABI sannan za a sake mata paspo, amma wai har yanzu ba ayi masu laifi ba.
To amma babu mamaki tunda malamai ma baka jin bakin su saboda karancin masu magana akan matsalolin a cikin su ko dai wacce ta shafi addini kai tsaye ko kuma wacce ta shafi gyaran al'umma. Kila su da ruwan su da APC ne, ni kuma na tabbata KAHUTU RARARA MAWAKI, ya fi su daraja a APCin!
Zamanin Goodluck Kiristanci ne ya mulke mu. Muma yanzu idan muka ce adalci ne Musulunci ya mulki kowa munyi DAI-DAI. Kodayake su fa rigar musulunci ne kawai a jikin su, da yin amfani da shi domin a samu matsayi da mukami, To amma tunda sakarcin mu yasa bazamu ce ba, me ya hana muyi magana a inda aka cuce mu? Gashi bamu yi maganar ba, kuma gashi Osinbanjo, da kan shi, yana cewa Kiristoci da yan kudu su suka fi kowa morar wannan gwamnatin. Dama kafin ya fadi mu munsan haka.
A waccen gwamnatin munci wuya, a wannan kuma zamu tashi a tutar babu.
Anya mu muminai ne kuwa?
Salisu Hassan Webmaster
12.03.2018

Post a Comment (0)