RIƘON AMANA A AIYUKAN ALBASHI


*Riƙon Amana A Ayyukan Albashi*

*✍️ Yusuf Lawal Yusuf*

Haƙiƙa a tsarin aikin albashi, akwai rubutattun ƙa'idojin aiki wanda yake yarjejeniya ce tsakanin wanda aka ɗauka aikin da wanda ake yi ma aikin. Har ma mutum sai ya rubuta takardar amincewa da hannun sa (bada keken rubutu ba) a waɗansu wuraren kafin ya fara aikin. To wajibi ne akansa ya kiyaye waɗannan ƙa'idojin saboda albashin da yake karɓa ya zama halas ɗin sa ne tsantsa. Ma'aikaci ta sani gwargwadon kiyaye amanar aikin sa gwargwadon halascin albashin sa. Ka sani cewa Manzon Allah (SAW) yace: "duk tsokar da ta ginu da haram, to wuta tafi cancanta da ita".

Yana daga cikin cin Amana rashin cika mudu a wajen aiki. Allah (SWT) Yace: "Azaba ta tabbata ga masu tauye mudu. Waɗanda idan su za su auna a wajen mutane za su nemi a cika musu. Idan kuma suka zo aunarwa sai su tauye mudu/ma'auni. Wai waɗannan basu sakankance cewa za'a tashe su ba ne? A wani yini (wanda yake al'amarinsa) mai girma?
Suratut Taɗfeef (1-5).

Ya ɗan'uwa, ka ɗauki waɗannan ayoyi ka auna ma'aikatan albashi dasu zaka taras ma su yawaita ƙorafi ne da raina abin da ake basu. Da zarar aka ce an samu jinkiri ko an yanke wani abu na albashin, to babu sauran sukuni. Amma abin da zai baka mamaki ka zo kaga mafi yawa ƙarfe nawa ake zuwa aikin (ga masu zuwa), kuma ƙarfe nawa ake tashi? Yaya kuma ake yin aikin?

Mallamin makaranta ya sani, aikin shi ya bada ilimi da tarbiyya. Cin Amana ne a taras da mallami baya karantar da abin daya kamata, ko kuma a taras da shi yana ɓata tarbiyya yara, musamman makarantun ƴan mata.

Zaka taras yadda aikin ofis ya zama, zaka taras da mutum a kujerar sa, kuma ka zo masa ne da aikin sada akw biyan sa akai, amma ba za ayi maka ba sai ka bada wani abu! Ko a ɓoye fike ɗin ka, ko takardar ka, ko dai ayi ta jamaka rai wai bakayi komai ba! Inna Lillahi Wa inna Ilaihi raji'un. Irin badaƙalar da ake yi a ofisoshi daban-daban a ƙananan hukumomi da sauran su, idan aka bibiya kare ma ba zai ci ba. Kai ɗan Adam, abincin ka haram, abin shan ka haram, ka ciyar da iyalin ka da haran, to wacannan al'umma ina zata? Allah Ya bamu ikon gyarawa.

Tsakure daga cikin wata takarda (Riƙon Amana A Mu'amala) da Sheikh Khidir Ibrahim Ƙaura ya gabatar mana a washegarin babbar sallah, shekara ta 1440/2019. Allah ya ƙarawa malam imani, ikhlasi, lafiya, da basira.
Post a Comment (0)