MANUFOFIN ƘARA AURE


*_▪️📚 MANUFOFIN SHARI'AR MUSULUNCI 10 📚▪️_*

*_MANUFOFIN ƘARA AURE_*

*_✍️ Yusuf Lawal Yusuf_*

Kishi wata ɗabi'a ce da Allah Ya halicci mata akan ta. Bukhari ya ruwaito daga Nana A'isha tana cewa: "Ban taɓa yin kishi da wata mace ba, irin kishin da na yi da Khadijah, tare da cewa ban taɓa ganinta ba, saboda yadda na ji Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ambatonta". Kishi mai tsafta, shi ne: kishiya ta yi rige-rige da kishiyarta, wajan kyaytatawa mijinsu. Akwai hikimomi masu ɗimbin yawa da suka sa Shari'ar Musulunci ta yi umarni da ƙarin aure. Ga wasu daga ciki:

1) Musulunci ya yi kallo na adalci zuwa ga mata gabaki-ɗayansu, don haka sai ya tausaya musu, ya umarci maza su ƙara aure, saboda mata sun fi maza yawa, idan har kowa ya tests a mace guda, ina za a kai matan da mazajensu suka mutu, da waɗanda aka saka.

2) Allah Ya azurta wasu mazan da tsananin sha'awa, don haka za su iya shiga wani hali duk lokacin da matarsu take haila ko kuma ta haihu, sai Allah Ya halatta sama da mace ɗaya, don kar namiji ya faɗa cikin haramun.

3) Wani lokacin za ka ga mutum ya auri matar da ba ta haihuwa. Idan har ba a halatta ƙarin aure ba, sai mutum ya mutu ba shi da zurriyar da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi zai yi alfahari da ita ranar Alƙiyama.

4) Wani lokacin mace ta kan yi doguwar rashin lafiya, ta yadda mijinta ba zai iya amfana da ita ba. In har ba a halatta sama da mace ɗaya ba, sai dai ya sake ta kenan ya auro wata! Amma idan akwai wata, zai iya haƙuri, ya ci gaba da zama da ita a haka.

5) Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana so ya yi alfahari da yawan al'ummarsa ranar Alƙiyama. Mata kuma yawancinsu daga sun wuce shekaru hamsin sai su daina haihuwa, saɓanin namiji, hakan sai ya nuna idan aka ba shi damar ya ƙara aure, zai haifi ƴaƴa da yawa tun da shi ba ya gajiyawa da wuri.

6) Wata kishiyar za ta iya zama hutu ga kishiyarta wajan ayyukan gida.

7) Allah Maɗaukakin Sarki shi ne wanda Ya halatta ƙarin aure: Yafi kowa sanin hikimar yin hakan. Saboda haka, ya kamata a sallamawa hukuncinSa.

Duba: Ahkamu Atta'addud fi Dhau'il Kitabi was Sunnah, shafi na 32.

Tsakure daga cikin littafin Manufofin Shari'ar Musulunci, wallafar Sheikh Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.

*_10th Rajab, 1442H (22/02/2021)_*
Post a Comment (0)