SAHABBAI SU NE FITILUN MUSULUNCI


*SAHABBAI SUNE FITILUN MUSULUNCI.*
-
GABATARWA:
Muhammad Umar Baballe.
-
"Haƙiƙa babu wata iriyar gwagwarmayar da sahabbai basu yi ta ba wajen ganin sun ɗaukaka wannan addinin na musulunci, sun sadaukar da jininsu, dukiyarsu, ƙarfin su, sunyi duk abinda suke iyawa domin ganin sun tabbatar da wannan addinin na Allah"
-
"Sun bashi kariya fiyeda ƙarfin iyawarsu idan akwai abinda yafi hakan, sun taimakawa Manzon Allah sallallahu alaihi wasallama wajen yaɗa shi a daidai lokacin da kafirai suke yunƙurin daƙile shi, sun haskaka shi a daidai lokacin da kafirai suke ƙoƙarin kifar dashi"
-
"Duk dalilin wannan aikin nasu abin yabo, Allah maɗaukakin sarki sai yayi musu kuɗin goro jimlatan-wahidah, sai yace ya yarda dasu, sannan kuma suma ɗin sun yarda dashi"
-
"Allah buwayi yace da dukkanin ilahirin sahabban da suka je yaƙin badar, baki ɗayanku kuyi duk abinda kuka ga dama, domin ni Allah haƙiƙa na gafarta muku"
-
"To! Yanzu da wannan dalilin mun fahimci cewa lallai su sahabbai sunyi abinda suka cancanci samun wannan kyautar daga gurin Allah maɗaukakin sarki tareda rahamarsa"
-
"Domin acikinsu an kashe wasu ta hanyar azabtarwa da wuta, wasu ta hanyar tsirewa, wasu kuma ta hanyar yankawa, duk badon komai ba sai don sunyi imani da wannan addinin na musulunci, sunce sai sun haskaka addinin musulunci"
-
"Amma tareda hakan wasu daga cikin mu suke zaginsu, suke muzanta su, suke faɗar munanan kalamai na rashin ladabi akansu, sun manta da irin ƙoƙarin da suka yiwa wannan addinin, sun manta da irin gwagwarmayar da suka sha wajen ɗaukaka wannan addinin, sun manta da irin wahalar da suka ɗauke duk don akan wannan addinin"
-
"Ko babu komai ai bai kyautu ace muna zaginsu ba, domin sune fitilun wannan addinin namu na musulunci, in ba domin Allah ya sanya ragamar addinin nan acikin zuƙatansu sun raine shi ba, da tuni bamu san irin halinda muke ciki ba a yanzu wallahi, wata-ƙila ma da tuni mu maguzawa ne, amma dalilin shiriyarsu, sai Allah ya sanya muma muka shiryu muka san addinin mu na musulunci"
-
Ya Allah kayi daɗin rahamarka da yardar ka akan waɗannan zaratan bayin naka, abokanan Manzon ka, mataimakan addininka, Ameen ya Allah.
-
✍🏿Muhammad Umar Baballe
Post a Comment (0)