*SALLAR KASARU.*
https://chat.whatsapp.com/LRPQDrs7qSoKXuSspoPkFm
*TAMBAYA*❓
Assalamu Alaikum Malam Dan Allah Inason amin bayani akan Sallar Kasaru. Allah yakara basira Nagode.
*AMSA*👇
Wa'alaikis Salam.
Amsa:Sallar Kasaru Sallah ne Wanda Akeyinta a lokacin da kikayi Tafiya diga garin da kike zuwa wani Gari. Indai misali za'a zo gidan Ku a tambayeki ina kike ko ina kika tafi ne? ace ai kinyi tafiya ne, bawai kinje unguwa ba. To zakiyi kasaru. Kuma in tafiyar yakai km46 anayin Kasaru. Manzon Allah saw yayi Kasaru, Kasaru Sauki ne ga musulmai masuyin Sallah daman shi Addinin Allah a koda yauce mai sauki ne saidai in bakisan yaya zakiyi shi ba sai kiga akwai wahala. In kinyi Kasaru a yayin da kike tafiyar ki kin samu lada, kuma kinyi koyi da Ma aikin Allah ne.
Amma fa ba ko wani tafiya ne zakiyi Mai kasaru ba. In tafiyar nan baishafi na Allah a ciki ba barakiyi kasaru ba. Misali wasu in zasuje party ko fashi ko wani aikin Alfasha a wani Gari babu kasaru a Kansu ko sunyi kasaru a hanya to su tabbata Sallar su bai cika ba Suketa kawai. Sannan Kasarun kwana nawa akeyinta? Akwai Sabanin maluma akan iya kwana kin da akeyi na kasaru. Na farko akwai malaman da suka tafi akan cewa indai kinyi kwana 4 ko 5 a garin da kikaje. To kasaru ya sauka a kanki zaki ci gaba da cika Sallah. Akwai Masu cewa in kinyi kwanaki 15, ko 18 a garin to Kasaru ya sauka a kanki zaki cika Sallar ki. Akwai kuma masu cewa iya kwanakin da duk zaki a wajen duk zakiyi tayin Kasaru ne har ki dawo garin da kike kafin nan Kasaru zai sauka a kanki. To Wallahu Alamu. Amma mun tafi akan in kin yi kwana ki 4 ko biyar ko 15, indai Wannan kwana kin sun cika kuma baki dawo ba. To ki cika Sallar ki shine zance mafi inganci.
Sallar Karasu diga lokacin da kikayi niyyar barin garin da kike zuwa garin da zakije zaki dauki niyyar duk Sallar da ya same ki a hanya zakiyi Kasaru, Sallar Azahar zaki mai dashi Raka'a 2 ne, Sallar La'asar shima zakiyi Raka'a 2, Magariba zaki kawo su dukka 3, Isha'i zakiyi 2 ne, Asubahi zaki kawo su dukka 2. Ba'a rage sallar Asubahi da magariba da sunayin Kasaru. Sannan indai zaki bi Sallar Jam'i ne, misali kinji Ana Sallah a wani Masallaci sai kikace bari ki bi su. To anan zaki ajiye Kasarun ki, zaki cika sallar ki kaman yadda zasu cika nasu. Kuma kada kice ke bara ki bi Jam'i ba sai kin bari sun idar da nasu kema kice zaki naki dabam saboda ke kina Kasaru, kin sabawa koyarwa ta Sunnar Annabi Saw, zaki bi su a lokacin kuma zakiyi Sallar ne kaman yadda zasuyi nasu. ba Kasaru ba. Ka da kaman Misali zaki bisu Sallar Azahar ke kice Kasaru kikeyi bari ki bi su Sallah, lokacin da Liman yayi zaman tahiya na farko sai suka tashi ke kuma kina zaune kina jiran su, su ciko sauran biyun kuyi Sallama tare in kinyi haka kin Sabawa Annabi. Indai zaki bi Sallar ma zauna Gari to zaki cika Sallar ki. Amma in ke kadai zakiyi Sallar ki to zaki yi Kasaru ne. Inda misali kene zakiyi Liman shi, kaman yadda maza sukeyi kuma tare da ma zauna garin toh nan kan zakiyi Kasaru. In yaso kina Sallama sai su kuma su tashi su cika Sallar Su.
Wallahu Tala Wa'ala Wa Alam.
Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕